circa 800–400 BC
The Hebrew Prophets
God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Irmiya 17:23kusan 611 K.H.
Duk da haka ba su saurara ba, ba su kuwa mai da hankali ba; suka taurare ba su kuwa saurara ko su karɓi horo ba.
- Irmiya 17:24kusan 611 K.H.
Amma in kuka yi hankali kuka yi mini biyayya, in ji Ubangiji, ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofi a ranar Asabbaci ba, amma kuka kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba tare da yin wani aiki a cikinta ba,
- Irmiya 17:25kusan 611 K.H.
sa’an nan sarakuna da suke zama a kursiyin Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan birni tare da fadawansu. Su da fadawansu za su shiga a kan kekunan yaƙi da kuma a kan dawakai, mutanen Yahuda suna musu rakiya tare da waɗanda suke zaune a Urushalima, wannan birni kuwa za tă kasance da mazauna har abada.
- Irmiya 17:26kusan 611 K.H.
Mutane za su zo daga garuruwan Yahuda da ƙauyukan kewaye da Urushalima, daga iyakar Benyamin da gindin tuddan yamma, daga ƙasar tudu da kuma Negeb, suna kawo hadayun ƙonawa da hadayun gari, sadakokin turare da na godiya zuwa gidan Ubangiji.
- Irmiya 17:27kusan 611 K.H.
Amma in ba ku yi mini biyayya ba, ba ku kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba, kuka ɗauki wani kaya yayinda kuke shiga ƙofofin Urushalima a ranar Asabbaci, to, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wutar da ba a iya kashewa, tă cinye kagaranta.’ ”
Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji.
- Irmiya 18:2kusan 608 K.H.
“Ka gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, a can zan ba ka saƙona.”
- Irmiya 18:3kusan 608 K.H.
Sai na gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, na gan shi yana aiki a na’urar ginin tukwanen.
- Irmiya 18:4kusan 608 K.H.
Amma tukunyar da yake ginawa ta lalace a hannuwansa, sai mai ginin tukwanen ya sāke gina wata tukunya dabam, yana gyara ta yadda ya ga dama.
- Irmiya 18:5kusan 608 K.H.
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
- Irmiya 18:6kusan 608 K.H.
“Ya gidan Isra’ila, ashe, ba zan yi da ku yadda mai ginin tukwanen nan yake yi ba?” In ji Ubangiji. “Kamar yumɓu a hannun mai ginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya gidan Isra’ila.
- Irmiya 18:7kusan 608 K.H.
A duk lokacin da na yi shela cewa za a tumɓuke, a kakkarya a kuma hallaka wata al’umma ko mulki,
- Irmiya 18:8kusan 608 K.H.
in wannan al’ummar da na yi wa gargaɗi ta tuba daga muguntarta, sai in janye in kuma fasa kawo mata masifar da na yi niyya aukar mata.
- Irmiya 18:9kusan 608 K.H.
In kuma wani lokaci na yi shela cewa za a gina wata al’umma ko mulki a kuma kafa ta,
- Irmiya 18:10kusan 608 K.H.
in ta yi mugunta a gabana ba tă kuwa yi mini biyayya ba, sai in janye alherin da na yi niyya in yi mata.
- Irmiya 18:11kusan 608 K.H.
“Yanzu fa, sai ka faɗa wa mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa ga shi! Ina shirya muku masifa ina ƙirƙiro dabara a kanku. Saboda haka ku juya daga mugayen hanyoyinku, kowannenku, ku canja hanyoyinku da kuma ayyukanku.’
- Irmiya 18:12kusan 608 K.H.
Amma za su amsa su ce, ‘Ba amfani. Za mu ci gaba da shirye-shiryenmu; kowannenmu zai bi taurin muguwar zuciyarsa.’ ”
- Irmiya 18:13kusan 608 K.H.
Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku tattambaya a cikin al’ummai. Wa ya taɓa jin irin wannan abu? Budurwa Isra’ila ta yi mugun abu mafi banƙyama.
- Irmiya 18:14kusan 608 K.H.
Dusar ƙanƙarar Lebanon ta taɓa rabuwa da kan duwatsun Lebanon? Ruwan mai sanyinsa daga rafuffukansa masu nesa sun taɓa daina gudu?
- Irmiya 18:15kusan 608 K.H.
Duk da haka mutanena sun manta da ni; sun ƙone turare wa gumaka marasa amfani, waɗanda suka sa su tuntuɓe a al’amuransu a hanyoyin dā. Sun sa suka yi tafiya a ɓarayin hanyoyi a hanyoyin da ba a gina ba.
- Irmiya 18:16kusan 608 K.H.
Ƙasarsu za tă zama kufai, abin reni har abada; dukan waɗanda suka wuce za su yi mamaki su kaɗa kai.
- Irmiya 18:17kusan 608 K.H.
Kamar iska daga gabas zan warwatsa su a gaban abokan gābansu; zan juya musu bayana, ba zan nuna musu fuskata ba a ranar masifarsu.”
- Irmiya 18:18kusan 608 K.H.
Suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya; gama koyarwar doka da firist ya yi ba za tă ɓace ba, haka ma shawara daga mai hikima da kuma magana daga annabawa. Saboda haka ku zo, mu fāɗa masa da harsunanmu kada mu saurari wani abin da zai faɗa.”
- Irmiya 18:19kusan 608 K.H.
Ka saurare ni, ya Ubangiji ka ji abin da masu zargina suke cewa!
- Irmiya 18:20kusan 608 K.H.
Ya kamata a sāka wa alheri da mugunta? Duk da haka sun haƙa mini rami. Ka tuna cewa na tsaya a gabanka na kuma yi magana a madadinsu don ka janye fushinka daga gare su.