Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Yohanna 4:3kusan 90 M.

    Amma duk ruhun da bai yarda da Yesu ba, ba daga Allah ba ne, ruhun magabcin Kiristi ne, wanda kuka ji yana zuwa, har ma ya riga ya shigo duniya.

  2. 1 Yohanna 4:4kusan 90 M.

    Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma.

  3. 1 Yohanna 4:5kusan 90 M.

    Su daga duniya ne saboda haka suke magana yadda duniya take ganin abubuwa, duniya kuwa tana sauraronsu.

  4. 1 Yohanna 4:6kusan 90 M.

    Mu daga Allah ne, kuma duk wanda ya san Allah yakan saurare mu. Amma duk wanda ba daga Allah ba, ba ya sauraronmu. Ta haka ne muke gane Ruhun gaskiya, da kuma ruhun ƙarya.

  5. 1 Yohanna 4:7kusan 90 M.

    Abokaina ƙaunatattu, mu ƙaunaci juna, domin ƙauna tana zuwa daga Allah ne. Duk mai ƙauna, haifaffe ne na Allah, ya kuma san Allah.

  6. 1 Yohanna 4:8kusan 90 M.

    Duk wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba, domin Allah ƙauna ne.

  7. 1 Yohanna 4:9kusan 90 M.

    Ga yadda Allah ya nuna ƙaunarsa a cikinmu, Allah ya aiki makaɗaici Ɗansa zuwa duniya domin mu rayu ta wurinsa.

  8. 1 Yohanna 4:10kusan 90 M.

    Wannan ita ce ƙauna, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa yă zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu.

  9. 1 Yohanna 4:11kusan 90 M.

    Abokaina ƙaunatattu, da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ya kamata mu ma mu ƙaunaci juna.

  10. 1 Yohanna 4:12kusan 90 M.

    Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu, ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan.

  11. 1 Yohanna 4:13kusan 90 M.

    Mun san cewa muna rayuwa a cikinsa shi kuma a cikinmu, domin ya ba mu Ruhunsa.

  12. 1 Yohanna 4:14kusan 90 M.

    Mun gani, mun kuma shaida cewa Uba ya aiko Ɗansa domin yă zama Mai Ceton duniya.

  13. 1 Yohanna 4:15kusan 90 M.

    Duk wanda ya yarda cewa Yesu Ɗan Allah ne, Allah yana raye a cikinsa, shi kuma a cikin Allah.

  14. 1 Yohanna 4:16kusan 90 M.

    Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana. Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa.

  15. 1 Yohanna 4:17kusan 90 M.

    Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shari’a, domin a wannan duniya muna kama da shi.

  16. 1 Yohanna 4:18kusan 90 M.

    Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.

  17. 1 Yohanna 4:19kusan 90 M.

    Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko.

  18. 1 Yohanna 4:20kusan 90 M.

    Duk wanda ya ce, “Ina ƙaunar Allah,” amma yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne. Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba.

  19. 1 Yohanna 4:21kusan 90 M.

    Ya kuma ba mu wannan umarni cewa duk wanda yake ƙaunar Allah, dole yă ƙaunaci ɗan’uwansa.

  20. 1 Yohanna 5:1kusan 90 M.

    Kowa ya gaskata cewa Yesu shi ne Kiristi, shi haifaffe na Allah ne, kuma duk mai ƙaunar mahaifi kuwa, yakan ƙaunaci ɗansa ma.

  21. 1 Yohanna 5:2kusan 90 M.

    Ga yadda muka san cewa muna ƙaunar ’ya’yan Allah. Muna yin haka ta wurin ƙaunar Allah da kuma aikata umarnansa.

  22. 1 Yohanna 5:3kusan 90 M.

    Ƙaunar Allah ita ce, a yi biyayya da umarnansa. Umarnansa kuwa ba masu nauyi ba ne;

  23. 1 Yohanna 5:4kusan 90 M.

    domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya.

  24. 1 Yohanna 5:5kusan 90 M.

    Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.

  25. 1 Yohanna 5:6kusan 90 M.

    Ga wanda ya zo ta wurin ruwa da jini, wato, Yesu Kiristi. Bai zo ta wurin ruwa kaɗai ba, sai dai ta wurin ruwa da kuma jini. Ruhu ne kuwa yake ba da shaida, gama Ruhu shi ne gaskiya.