Tsallake zuwa abun ciki

Hebron

56 verses

31.5300, 35.0900 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Hebron

Tace bisa littafi
  1. Dawuda kuma ya tafi tare da dukan mutanen da suke tare da shi, kowa da iyalinsa, suka zauna a Hebron da garuruwansa.

  2. Tsawon lokacin da Dawuda ya yi mulki a Hebron a kan gidan Yahuda, shekara bakwai ne da wata shida.

  3. Suka ɗauki gawar Asahel suka binne a kabarin mahaifinsa a Betlehem. Sa’an nan Yowab da mutanensa suka bi dare har suka iso Hebron da safe.

  4. An haifa wa Dawuda ’ya’ya maza a Hebron. Ɗansa na fari shi ne Amnon, ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel;

  5. na shida kuma shi ne Itireyam, ɗan Egla matar Dawuda. An haifi waɗannan wa Dawuda a Hebron.

  6. Abner kuma ya yi magana da mutane Benyamin da kansa. Sa’an nan ya tafi Hebron yă gaya wa Dawuda ko mene ne Isra’ila da kuma dukan gidan Benyamin suke so su yi.

  7. Sa’ad da Abner wanda yake tare da mutane ashirin suka zo wurin Dawuda a Hebron, Dawuda ya shirya masa liyafa tare da mutanensa.

  8. Ba a jima ba sai mutanen Dawuda da Yowab suka dawo daga hari. Suka kawo ganima da yawa tare da su. Abner kuwa ya riga ya bar Dawuda a Hebron, domin Dawuda ya sallame shi, shi kuma ya tafi lafiya.

  9. To, da Abner ya komo Hebron, Yowab ya ratse da shi zuwa hanyar shigar gari kamar zai gana da shi a kaɗaice. Amma a can ya soki Abner a ciki, ya kashe shi don yă rama mutuwar ɗan’uwansa Asahel.

  10. Suka binne Abner a Hebron, sarki kuwa ya ɗaga murya ya yi kuka a kabarin Abner.

  11. Sa’ad da Ish-Boshet ya ji labari cewa Abner ya mutu a Hebron, sai ya karaya, sai dukan hankalin Isra’ila ya tashi.

  12. Suka kawo kan Ish-Boshet wa Dawuda a Hebron, suka ce wa sarki, “Ga kan Ish-Boshet ɗan Shawulu, maƙiyinka, wanda ya nemi yă kashe ka. A yau Ubangiji ya rama wa ranka yă daɗe sarki, a kan Shawulu da zuriyarsa.”

  13. Saboda haka Dawuda ya umarci mutanensa, suka kuwa kashe su. Suka yayyanka hannuwansu da ƙafafunsu, suka kuma rataye jikunansu kusa da tafki a Hebron. Amma suka ɗauki kan Ish-Boshet suka binne a kabarin Abner a Hebron.

  14. Dukan kabilar Isra’ila suka zo wurin Dawuda a Hebron suka ce, “Mu nama da jininka ne.

  15. Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, sarki ya yi yarjejjeniya da su a gaban Ubangiji, suka kuwa naɗa Dawuda sarki bisa Isra’ila.

  16. A Hebron ya yi mulki a bisa Yahuda shekara bakwai da wata shida, a Urushalima kuma ya yi mulki a bisa Isra’ila da Yahuda shekara talatin da uku.

  17. Bayan ya bar Hebron, Dawuda ya ƙara ɗauko wa kansa waɗansu ƙwarƙwarai da mata a Urushalima. Aka haifa masa ’ya’ya maza da mata.

  18. A ƙarshen shekara huɗu, Absalom ya ce wa sarki, “Bari in tafi Hebron in cika alkawarin da na yi wa Ubangiji.

  19. Sarki ya ce, “Ka sauka lafiya.” Sai ya tafi Hebron.

  20. Sai Absalom ya aiki manzanni a asirce cikin dukan kabilan Isra’ila, ya ce musu su ce, “Da zarar kuka ji an busa ƙaho, sai ku ce, ‘Absalom sarki ne a Hebron.’ ”

  21. Ya yi sarauta shekaru arba’in a bisa Isra’ila. Wato, shekaru bakwai a Hebron da kuma talatin da uku a Urushalima.

  22. Waɗannan su ne ’ya’yan Dawuda maza da aka haifa masa a Hebron. Ɗan farinsa shi ne Amnon ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel; na biyun, Daniyel ɗan Abigiyel mutuniyar Karmel;

  23. Waɗannan su ne aka haifa wa Dawuda a Hebron, inda ya yi mulki shekaru bakwai da wata shida. Dawuda ya yi mulki a Urushalima shekaru talatin da uku,

  24. Aka ba su Hebron a Yahuda tare da wuraren kiwon da suke kewayenta.

  25. Saboda haka aka ba wa zuriyar Haruna Hebron (birnin mafaka), da Libna, Yattir Eshtemowa,