Jesus
An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ
Ayoyin da suka ambaci Jesus
Na san kullum kakan saurare ni, na dai faɗa haka ne saboda amfanin mutanen nan da suke tsaitsaye, don su gaskata cewa kai ka aiko ni.”
Sa’ad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Lazarus, ka fito!”
Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a daure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi. Yesu ya ce musu, “Ku tuɓe kayan bizo, ku bar shi yă tafi.”
Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo don su ziyarci Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi.
Amma waɗansunsu suka je wurin Farisiyawa suka gaya musu abin da Yesu ya yi.
Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira taron Majalisa. Suka yi tambaya suna cewa, “Me muke yi ne? Ga mutumin nan yana yin abubuwan banmamaki masu yawa.
In fa muka ƙyale shi ya ci gaba da haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma su zo su karɓe wurinmu su kuma ƙwace ƙasarmu.”
Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa,
ba don ƙasan nan kaɗai ba amma don yă tattaro ’ya’yan Allah da suke warwatse ma, su zama ɗaya.
Saboda haka, daga wannan rana suka ƙulla su ɗauke ransa.
Saboda haka Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba. A maimako haka sai ya janye zuwa yankin kusa da hamada, a wani ƙauye da ake kira Efraim, inda ya zauna da almajiransa.
Suka yi ta neman Yesu, da suke a tsaitsaye a filin haikali kuwa suka dinga tambayar juna, suna cewa, “Me kuka gani? Anya, zai zo Bikin kuwa?”
Manyan firistoci da Farisiyawa tuni sun riga sun yi umarni cewa duk wanda ya san inda Yesu yake, yă faɗa don su kama shi.
Kwana shida kafin Bikin Ƙetarewa, sai Yesu ya iso Betani, inda Lazarus yake, wanda Yesu ya tā da daga matattu.
A nan aka shirya abincin yamma don girmama Yesu. Marta ta ce yi hidima, Lazarus kuma yana ɗaya cikin waɗanda suke ci tare shi.
Sai Maryamu ta ɗauki wajen awo guda na nardi zalla, turare mai tsada; ta zuba a ƙafafun Yesu ta kuma goge ƙafafunsa da gashinta. Gidan duk ya cika da ƙanshin turaren.
Amma ɗaya daga cikin almajiransa, Yahuda Iskariyot, wanda daga baya zai bashe shi, bai amince ba ya ce,
Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta, an nufa ta ajiye wannan turaren don ranar jana’izata.
Kullum za ku kasance da matalauta, amma ba kullum za ku kasance tare da ni ba.”
Ana cikin haka sai babban taron Yahudawa suka sami labari Yesu yana can suka kuwa zo, ba kawai don shi ba amma don su kuma ga Lazarus, wanda ya tā da daga matattu.
gama dalilinsa Yahudawa da yawa suna komawa ga Yesu suna kuma ba da gaskiya gare shi.
Kashegari babban taron da suka zo Bikin suka sami labari cewa Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima.
Sai suka ɗaɗɗauko rassan dabino suka fiffita taryensa, suna ɗaga murya suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Mai albarka ne Sarkin Isra’ila!”
Yesu ya sami ɗan jaki, ya hau, kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Kada ki ji tsoro, ya Diyar Sihiyona; duba, ga sarkinki yana zuwa, zaune a kan aholaki jaki.”