God
Ayoyin da suka ambaci God
Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da mugayen siffofi ko kuma da wani daga laifofinsu ba, gama zan cece su daga dukan zunubinsu na ridda, zan kuma tsarkake su. Za su zama mutanena, ni kuma zan zama Allahnsu.
“ ‘Bawana Dawuda zai zama sarki a kansu, dukansu kuwa za su kasance da makiyayi guda. Za su bi dokokina su kuma kiyaye ƙa’idodina.
Za su zauna a ƙasar da na ba wa bawana Yaƙub, ƙasar da kakanninsu suka zauna. Su da ’ya’yansu da ’ya’ya ’ya’yansu za su zauna a can har abada, kuma Dawuda bawana zai zama sarkinsu har abada.
Zan yi alkawarin salama da su; zai zama madawwamin alkawari. Zan kafa su in ƙara yawansu, zan kuma sa wuri mai tsarkina a cikinsu har abada.
Mazaunina zai kasance da su; zan kuwa zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena.
Sa’an nan al’ummai za su san cewa Ni Ubangiji na mai da Isra’ila mai tsarki, sa’ad da wuri mai tsarkina yana a cikinsu har abada.’ ”
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal.
Zan juyar da kai, in sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka in fitar da kai tare da dukan sojojinka, dawakanka, mahayan dawakanka saye da makamai, da kuma jama’a mai girma masu riƙe da garkuwoyi manya da ƙanana, dukansu da takuba a zāre.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar, tunani zai shiga cikin zuciyarka za ka kuma ƙirƙiro muguwar dabara.
Za ka ce, “Zan kai hari wa ƙasar da ƙauyukanta ba su da katanga; zan fāɗa wa mutanen da suke zamansu kurum cikin salama, dukansu suna zama babu katanga babu ƙofofi ko ƙyamare.
“Saboda haka ɗan mutum, ka yi annabci ka ce wa Gog, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar, sa’ad da mutanena Isra’ila suna zaman lafiya, ba za ka sani ba?
Za ka ci gaba a kan mutanena Isra’ila kamar yadda girgijen yakan rufe ƙasa. A kwanaki masu zuwa, ya Gog, zan kawo ka, ka yi yaƙi da ƙasata, domin al’ummai su san ni sa’ad da na nuna kaina mai tsarki ta wurinka a gabansu.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba kai ba ne na yi magana da kai a kwanakin dā ta wurin bayina annabawan Isra’ila? A lokacin sun yi annabci shekaru masu yawa cewa zan kawo ka, ka yaƙe su.
Ga abin da zai faru a ranar. Sa’ad da Gog ya fāɗa wa ƙasar Isra’ila, fushina mai zafi zai ƙuna, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Cikin kishina da hasalata mai zafi zan furta cewa a wannan lokaci za a yi babbar girgizar ƙasa a ƙasar Isra’ila.
Kifin teku, tsuntsayen sarari, namun jeji, kowace halitta mai rarrafe da kuma dukan mutane a duniya za su yi rawar jiki a gabana. Za a tumɓuke duwatsu, a ragargaza tsaunuka, kuma kowane bango zai fāɗi ƙasa.
Zan kira takobi a kan Gog a dukan duwatsuna, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Kowane takobin mutum zai yi gāba da ɗan’uwansa.
Zan yi hukunci a kansa da annoba da kuma zub da jini; zan yi ruwa mai yawa da ƙanƙara da kibiritu mai cin wuta a kansa da a kan sojojinsa da kuma a kan al’ummai masu yawa da suke tare da shi.
Ta haka zan nuna girmana da kuma tsarkina, zan sanar da kaina a gaban al’ummai masu yawa. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’
“Ɗan mutum, ka yi annabci a kan Gog ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal.
Zan juya ka in kuma ja ka. Zan kawo ka daga can arewa in aike ka don ka fāɗa wa duwatsun Isra’ila.
Sa’an nan zan karya bakan da take a hannun hagunka, in sa kibiyoyin da suke a hannun damanka su fāɗi.
A kan duwatsun Isra’ila za ka fāɗi, kai da sojojinka da kuma al’ummai da suke tare da kai. Zan bayar da kai ka zama abinci ga tsuntsaye da namun jeji masu cin nama.
Za ka mutu a fili, gama haka ni na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.