God
Ayoyin da suka ambaci God
Amma na ce, “A, Ubangiji Mai Iko Duka, annabawa sun riƙa ce musu, ‘Ba za ku ga takobi ko ku yi fama da yunwa ba. A maimako, zan ba ku madawwamiyar salama.’ ”
Sai Ubangiji ya ce mini, “Annabawa suna ta annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ban kuma naɗa su ba, ban yi musu magana ba. Suna muku annabci wahayin ƙarya, suna muku duba marar amfani, suna bautar gumaka suna kuma bayyana tunanin kansu ne.
Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce game da annabawan da suke annabci da sunana. Ban aike su ba, duk da haka suna cewa, ‘Babu takobi ko yunwar da zai taɓa wannan ƙasa.’ Waɗannan annabawa takobi da yunwa za su hallaka su.
Mutanen da suke musu annabcin kuwa za a kore su zuwa titunan Urushalima saboda yunwa da kuma takobi. Babu wanda zai binne su, ko ya binne matansu, ko ’ya’yansu maza da mata. Zan aukar musu da masifar da ya dace da su.
“Ka yi musu wannan magana, “ ‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye dare da rana kada su daina; saboda ’yata budurwa, mutanena, sun sha wahalar babban rauni, an yi musu bugu mai ragargazawa.
In na shiga cikin ƙasar, na ga waɗanda takobi ya kashe; in na shiga cikin birni, na ga waɗanda suke fama da yunwa. Da Annabi da firist duk sun tafi ƙasar da ba su sani ba.’ ”
Ka ƙi Yahuda ɗungum ke nan? Kana ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu don kada mu warke? Mun sa zuciya ga salama babu abin alherin da ya zo, mun sa rai ga lokacin warkarwa amma sai ga razana.
Ya Ubangiji, mun gane da muguntarmu da kuma laifin kakanninmu; tabbatacce mun yi maka zunubi.
Saboda sunanka kada ka ƙi mu; kada ka ƙasƙantar da kursiyoyinka mai ɗaukaka. Ka tuna da alkawarinka da mu kada ka tā da shi.
Akwai wani daga cikin gumaka marasa amfani na al’ummai da ya kawo ruwan sama? Sararin sama kansu sukan yi yayyafi? A’a, kai ne, ya Ubangiji Allahnmu. Saboda haka sa zuciyarmu tana a kanka, gama kai ne kake yi wannan duka.
Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da Musa da Sama’ila za su tsaya a gabana, zuciyata ba za tă komo ga mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana! Su tafi!
In kuma suka tambaye ka, ‘Ina za mu tafi?’ Sai ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Waɗanda aka ƙaddara ga mutuwa, ga mutuwa za su; waɗanda aka ƙaddara ga takobi, ga takobi za su; waɗanda aka ƙaddara ga yunwa, ga yunwa za su; waɗanda aka ƙaddara ga zaman bauta, ga zaman bauta za su.’
“Zan aika musu da iri masu hallakarwa guda huɗu,” in ji Ubangiji, “takobi zai kashe, karnuka za su kwashe, tsuntsaye da namun jeji kuma su cinye su kuma hallaka.
Zan sa su zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya saboda abin da Manasse ɗan Hezekiya sarkin Yahuda ya aikata a Urushalima.
Kin ƙi ni,” in ji Ubangiji. “Ki ci gaba da ja da baya. Ta haka zan ɗibiya hannuwana a kanki in hallaka ki; ba zan ƙara nuna miki jinƙai ba.
Zan sheƙe ki da abin sheƙewa a ƙofofin birnin ƙasar. Zan kawo baƙin ciki da hallaka a kan mutanena, gama ba su canja hanyoyinsu ba.
Zan ƙara yawan gwaurayensu su fi yashin teku yawa. Da tsakar rana zan kawo mai hallakarwa a kan iyaye mata na samarinsu; farat ɗaya zan kawo musu wahala da razana.
Mahaifiya ’ya’ya bakwai za tă suma ta ja numfashinta na ƙarshe. Ranarta zai fāɗi tun lokacin bai yi ba; za tă sha kunya a kuma wulaƙanta ta. Zan sa a kashe raguwa da takobi a gaban abokan gābansu,” in ji Ubangiji.
Ubangiji ya ce, “Tabbatacce zan cece ka don alheri; tabbatacce zan sa abokan gābanka su yi roƙo gare ka a lokacin masifa da kuma lokacin wahala.
Ka gane, ya Ubangiji; ka tuna da ni ka kuma lura da ni. Ka yi mini ramuwa a kan masu tsananta mini. Cikin jimirinka, kada ka ɗauke ni; ka tuna yadda na sha zagi saboda kai.
Sa’ad da maganganunka suka zo, na cinye su; suka zama abin farin ciki zuciyata kuma ta yi murna, gama ana kirana da sunanka, Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki.
Ban taɓa zauna a cikin ’yan tawaye ba, ban taɓa yi murna da su ba; na zauna ni kaɗai domin hannunka yana a kaina ka kuma sa na cika da haushi.
Me ya sa wahalata ba ta ƙarewa mikina kuma ba ya warkuwa? Za ka zama mini kamar rafi mai yaudara ne, kamar maɓulɓulan da ta kafe ne?
Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “In ka tuba, zan maido da kai don ka bauta mini; in ka ambaci maganganu masu kyau, ba marasa kyau ba, za ka zama kakakina. Bari wannan mutane su juyo gare ka, amma kada ka juye gare su.
Zan mai da kai katanga ga wannan mutane, katanga mai ƙarfi na tagulla; za su yi yaƙi da kai amma ba za su yi nasara a kanka ba, gama ina tare da kai don in kuɓutar in kuma cece ka,” in ji Ubangiji.