Tsallake zuwa abun ciki

Balaam

59 ayoyi · 1 ɗan gida

Ayoyin da suka ambaci Balaam

Tace bisa littafi
  1. a can ya yi hadaya da shanu da tumaki, ya kuwa aika wa Bala’am da dattawan da suke tare da shi.

  2. Kashegari, Balak ya ɗauki Bala’am ya kai shi kan Bamot Ba’al, daga can ya iya ganin sassan sansanin Isra’ilawa.

  3. Bala’am ya ce, “Ka gina mini bagadai bakwai a nan, ka shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.”

  4. Balak ya yi yadda Bala’am ya faɗa, sai su biyu suka miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

  5. Sa’an nan Bala’am ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka, ni kuwa in koma wani wurin da yake a kaɗaice. Wataƙila Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Sai ya haura kan wani wurin da yake a kaɗaice a tudun.

  6. Allah kuwa ya sadu da Bala’am. Bala’am ya ce, “Na shirya bagadai bakwai, na kuma miƙa bijimi guda da rago guda, a kan kowane bagade.”

  7. Ubangiji ya ba wa Bala’am saƙo ya ce, “Ka koma wurin Balak, ka faɗa masa wannan saƙo.”

  8. Balak ya ce wa Bala’am, “Me ke nan ka yi mini? Na kawo ka, ka la’anta abokan gābana, sai ga shi albarka kake sa musu!”

  9. Ubangiji ya sadu da Bala’am, ya kuma ba shi saƙo ya ce, “Koma wurin Balak ka ba shi wannan saƙo.”

  10. Sai Balak ya ce wa Bala’am, “Kada ka la’anta su, kada kuma ka sa musu albarka!”

  11. Bala’am amsa ya ce, “Ban faɗa maka zan yi kaɗai abin da Ubangiji ya ce ba?”

  12. Sai Balak ya ce wa Bala’am, “Zo in kai ka wani wuri. Wataƙila zai gamshi Allah, yă bari ka la’anta mini su daga can.”

  13. Balak kuwa ya ɗauki Bala’am zuwa ƙwanƙolin Feyor, wanda yake fuskantar hamada.

  14. Bala’am ya ce, “Ka gina mini bagadai bakwai a nan, ka kuma shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.”

  15. Balak ya yi yadda Bala’am ya ce, ya kuwa miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

  16. To, da Bala’am ya ga cewa Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra’ila albarka, bai koma wajen sihiri kamar dā ba, amma ya juya fuskarsa wajen hamada.

  17. Da Bala’am ya duba sai ya ga Isra’ila sun yi sansani kabila, kabila, Ruhun Allah kuwa ya sauko masa,

  18. sai ya yi annabcinsa ya ce, “Maganar Bala’am ɗan Beyor, saƙon mutumin da idanunsa ke gani sarai,

  19. Fushin Balak ya ƙuna a kan Bala’am. Ya tafa hannunsa, ya ce masa, “Na kira ka don ka la’anta abokan gābana, amma sai ga shi ka sa musu albarka har sau uku.

  20. Bala’am ya ce wa Balak, “Ban faɗa wa ’yan aikan da ka aiko wurina ba cewa,

  21. Sa’an nan ya furta saƙonsa. “Maganar Bala’am ɗan Beyor, saƙon mutumin da idanunsa ke gani sarai,

  22. Sa’an nan Bala’am ya tashi ya koma gidan, Balak kuma ya yi tafiyarsa.

  23. A cikin waɗanda aka kashe kuwa akwai Ewi, Rekem, Zur, Hur da Reba; sarakuna biyar na Mediyawa. Suka kuma kashe Bala’am ɗan Beyor da takobi.

  24. Su ne waɗanda suka bi shawarar Bala’am suka kuma zama sanadin sa Isra’ilawa suka juya wa Ubangiji baya, har ya kawo abin da ya faru da Feyor, har annoba ya kashe dukan mutanen Ubangiji.

  25. Gama ba su zo sun tarye ku da burodi da ruwa a hanyarku, sa’ad da kuka fito daga Masar ba, sai ma suka yi haya Bala’am ɗan Beyor daga Fetor a Aram-Naharayim yă furta la’ana a kanku.