Tsallake zuwa abun ciki

Ahab

80 ayoyi · 6 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Ahab

Tace bisa littafi
  1. A shekara ta goma sha biyu ta Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra’ila, Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda ya fara mulki.

  2. Ya bi gurbin gidan Ahab, ya yi mugunta a gaban Ubangiji yadda gida Ahab ta yi, gama yana da dangantaka ta aure da gidan Ahab.

  3. Ahaziya ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab don su yaƙi Hazayel sarkin Aram a Ramot Gileyad. Arameyawa suka yi wa Yoram rauni;

  4. saboda haka Sarki Yoram ya koma zuwa Yezireyel don yă yi jinyar raunin da Arameyawa suka ji masa a Rama a yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sai Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel yă dubi Yoram ɗan Ahab domin an yi masa rauni.

  5. Za aka hallaka gidan Ahab maigidanka, zan kuma ɗauki fansar jinin bayina annabawa da kuma jinin dukan bayin Ubangiji da Yezebel ta zub da.

  6. Dukan gidan Ahab zai hallaka. Zan kashe dukan ’ya’yan Ahab maza a Isra’ila, bayi ko ’yantattu.

  7. Zan mai da gidan Ahab kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat da kuma kamar gidan Ba’asha ɗan Ahiya.

  8. Yehu ya ce wa Bidkar, hafsan keken yaƙinsa, “Ka ɗauke shi ka jefar a filin da yake na Nabot mutumin Yezireyel. Ka tuna yadda ni da kai muke a kekunan yaƙi a bayan Ahab mahaifinsa sa’ad da Ubangiji ya yi wannan annabci game da shi,

  9. (A shekara ta goma sha ɗaya ta Yoram ɗan Ahab, Ahaziya ya zama sarkin Yahuda.)

  10. To, akwai ’ya’ya maza saba’in na gidan Ahab a Samariya. Saboda haka Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika su Samariya, zuwa ga shugabannin Yezireyel, da kuma ga masu lura da ’ya’yan Ahab. Ya ce,

  11. Ku sani fa, ba kalmar da Ubangiji ya faɗa game da gidan Ahab da ba za tă cika ba. Ubangiji ya yi abin da ya alkawarta ta bakin bawansa Iliya.”

  12. Saboda haka Yehu ya kashe duk waɗanda suka rage na iyalin Ahab a Yezireyel, tare da dukan fadawansa da aminansa da firistocinsa, ba a bar masa kowa ba.

  13. Da Yehu ya isa Samariya, sai ya karkashe dukan sauran iyalin Ahab, ya hallaka su, bisa ga maganar da Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya.

  14. Sa’an nan Yehu ya tattara dukan jama’a ya ce musu, “Ahab ya bauta wa Ba’al kaɗan ne kawai; amma Yehu zai bauta masa sosai.

  15. Ubangiji ya ce wa Yehu, “Tun da yake ka aikata abin da yake mai kyau a idanuna, ka kuma yi wa gidan Ahab dukan abin da yake a zuciyata, ina yin maka alkawari cewa zuriyarka za su yi mulkin Isra’ila har tsara ta huɗu.”

  16. Ya sāke gina masujadan da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba’al bagadai. Ya kafa ginshiƙin Ashera kamar yadda Ahab sarkin Isra’ila ya yi. Ya durƙusa wa dukan rundunan taurari ya yi musu sujada.

  17. Zan auna Urushalima da ma’aunin da na yi amfani da shi a kan Samariya, zan kuma yi amfani da magwajin da na yi amfani da shi a kan gidan Ahab. Zan shafe Urushalima yadda mutum yake wanke kwano yă kife.

  18. Yanzu fa Yehoshafat ya wadace ƙwarai yana kuma da girma, ya kuma haɗa kansa da Ahab ta wurin aure.

  19. Bayan ’yan shekaru sai ya gangara don yă ziyarci Ahab a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki da shanu masu yawa dominsa da kuma mutanen da suke tare da shi, ya kuma lallashe shi yă yaƙi Ramot Gileyad.

  20. Ahab sarkin Isra’ila ya tambayi Yehoshafat sarkin Yahuda ya ce, “Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Ramot Gileyad?” Yehoshafat ya amsa ya ce, “Ni kamar kai ne, kuma mutanena kamar naka ne; za mu tafi tare da kai a yaƙin.”

  21. Ubangiji kuwa ya ce, ‘Wa zai ruɗe Ahab sarki Isra’ila zuwa yaƙi da Ramot Gileyad da kuma zuwa mutuwarsa a can?’ “Wani ya ba da wata shawara, wani kuma wata dabam.

  22. Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, kamar yadda gidan Ahab ta yi, gama ya auri ’yar Ahab. Ya aikata mugayen ayyuka a idon Ubangiji.

  23. Amma ka yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, ka sa Yahuda ya kauce, ka kuma sa mutanen Urushalima suka yi karuwanci, kamar yadda gidan Ahab ta yi. Ka kuma kashe ’yan’uwanka, membobi gidan mahaifinka, mutanen da suka fi ka kirki.

  24. Shi ma ya yi tafiya a hanyoyin gidan Ahab, gama mahaifiyarsa ta ƙarfafa shi yă yi abin da ba shi da kyau.

  25. Ya aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, yadda gidan Ahab ta yi, gama bayan mutuwar mahaifinsa, sai gidan Ahab ta zama masu ba shi shawara, shawarar da ta kai shi ga lalacewa.