Tsallake zuwa abun ciki

Ahab

80 ayoyi · 6 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Ahab

Tace bisa littafi
  1. Ana nan bayan haka sai waɗannan abubuwa suka faru. Nabot mutumin Yezireyel yana da gonar inabi a Yezireyel, a yankin Samariya, kusa da gidan Sarki Ahab.

  2. Sai Ahab ya ce wa Nabot, “Ka ba ni gonar inabinka in yi amfani da ita don kayan lambu, da yake tana kusa da fadana. Zan ba ka wata gonar inabin da ta fi wannan, ko kuma in ka gwammace, sai in biya ka duk abin da ya dace da ita.”

  3. Amma Nabot ya amsa wa Ahab ya ce, “Ubangiji yă sawwaƙe in ba ka gādon kakannina.”

  4. Ahab ya cika da fushi saboda Nabot, mutumin Yezireyel ya ce, “Ba zan ba ka gādon kakannina ba.” Ya kwanta a gadonsa yana zub da hawaye, ya kuma ƙi cin abinci.

  5. Sai ta rubuta wasiƙu a sunan Ahab, ta buga hatiminsa a kansu, sa’an nan ta aika su ga dattawa da manyan gari waɗanda suke zama a birnin da Nabot yake.

  6. Nan da nan sa’ad da Yezebel ta ji cewa an jajjefe Nabot da dutse ya kuma mutu, sai ta ce wa Ahab, “Tashi ka mallaki gonar inabin Nabot mutumin Yezireyel wanda ya ƙi ya sayar maka. Ba shi da rai, ya mutu.”

  7. Da Ahab ya ji cewa Nabot ya mutu, sai ya tashi ya gangara don yă mallaki gonar inabin Nabot.

  8. Ta ce, “Gangara don ka sadu da Ahab sarkin Isra’ila, wanda yake mulki a Samariya. Yanzu yana a gonar inabin Nabot, inda ya tafi yă mallake ta.

  9. Ahab ya ce wa Iliya, “Wato, ka same ni kuma, abokin gābana!” Sai ya amsa ya ce, “Na same ka, domin ka sayar da kanka ga yin mugunta a gaban Ubangiji.

  10. ‘Zan kawo masifa a kanka. Zan kawar da zuriyarka, in kuma yanke daga Ahab kowane ɗa namiji na ƙarshe cikin Isra’ila, bawa ko ’yantacce.

  11. “Karnuka za su cinye waɗanda suke na Ahab waɗanda suka mutu a cikin birni, tsuntsayen sararin sama kuma za su cinye waɗanda suka mutu a jeji.”

  12. (Babu wani mutum kamar Ahab, wanda ya ba da kansa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji. Yezebel matarsa ce ta zuga shi.

  13. Sa’ad da Ahab ya ji waɗannan kalmomi, sai ya yage rigarsa, ya sa rigunan makoki, ya kuma yi azumi. Ya kwanta a kayan makoki, ya kuma yi tafiya cikin sauƙinkai.

  14. “Ka lura da yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana kuwa? Domin ya ƙasƙantar da kansa, ba zan kawo wannan masifa a kwanakinsa ba, amma zan kawo ta a kan gidansa a kwanakin ɗansa.”

  15. Kuma Ubangiji ya ce, ‘Wa zai ruɗi Ahab zuwa yaƙi da Ramot Gileyad, yă kuma kai shi mutuwarsa a can?’ “Wani ya ce wannan, wani ya ce wancan.

  16. Game da sauran ayyukan mulkin Ahab, haɗe da dukan abin da ya yi, da fadan da ya gina ya kuma shimfiɗa da hauren giwa, da biranen da ya gina, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

  17. Ahab ya huta da kakanninsa. Ahaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  18. Yehoshafat ɗan Asa ya zama sarkin Yahuda a shekara ta huɗu ta Ahab sarkin Isra’ila.

  19. A lokacin Ahaziya ɗan Ahab ya ce wa Yehoshafat, “Bari mutanena su tafi tare da mutanenka,” amma Yehoshafat ya ƙi.

  20. Ahaziya ɗan Ahab ya zama sarkin Isra’ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta Yehoshafat sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila shekaru biyu.

  21. Bayan mutuwar Ahab, Mowab ta yi wa Isra’ila tawaye.

  22. Yoram, ɗan Ahab ya zama sarki Isra’ila, a Samariya, a shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yehoshafat, sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki shekara goma sha biyu.

  23. Amma bayan mutuwar Ahab, sai sarkin Mowab ya yi wa sarkin Isra’ila tawaye.

  24. A shekara ta biyar ta mulkin Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra’ila, sa’ad da Yehoshafat yake sarautar Yahuda, Yoram ɗan Yehoshafat, ya fara mulkinsa a matsayin sarkin Yahuda.

  25. Ya bi gurbin sarakunan Isra’ila, yadda gidan Ahab ta yi, gama ya auri ’yar Ahab. Ya yi mugunta a gaban Ubangiji.