Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Watchmen: Reported the approach of all strangers

10 ayoyi · 19 fannoni

Ayoyi game da Reported the approach of all strangers

  1. Yayinda Dawuda yake zaune tsakanin ƙofofin ciki da na waje, sai mai tsaro ya hau rufin ginin da yake kan hanyar shiga ta wajen katanga. Da ya duba sai ya ga wani mutum shi kaɗai yana gudu.

  2. Mai tsaro ya tā da murya ya faɗa wa sarki. Sarki ya ce, “In shi kaɗai ne, ya kawo labari mai kyau ke nan.” Mutumin ya matso kusa-kusa.

  3. Sai mai tsaron ya ga wani mutum yana zuwa a guje. Sai ya tā da murya ya kira mai tsaron ƙofa ya ce, “Duba, ga wani mutum kuma yana gudu shi kaɗai!” Sarki ya ce, “Shi ma yana kawo labari mai daɗi ne.”

  4. Sai mai tsaron ya ce, “A ganina gudu na farin, ya yi kama da gudun Ahimawaz, ɗan Zadok.” Sarki ya ce, “Shi mutumin kirki ne, yana zuwa da saƙo mai kyau.”

  5. Sai mahayin dokin ya hau, ya ruga, ya taryi Yehu, ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’ ” Sai Yehu ya ce masa, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.” Sai mai tsaron ya ce wa sarki, “Ɗan saƙon ya kai wurinsu, amma ba ya dawowa.”

  6. Saboda haka sarki ya sāke aika mahayin doki na biyu. Sa’ad da ya isa wurinsu sai ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’ ” Yehu ya ce, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.”

  7. Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma shi ma ba ya dawowa. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa kamar mahaukaci.”

  8. Ga abin da mai girma ya ce mini, “Tafi, ka sa mai tsaro ka kuma sa ya ba da rahoton abin da ya gani.

  9. Sa’ad da ya ga kekunan yaƙi tare da ƙungiyoyin dawakai, mahaya a kan jakuna, ko mahaya a kan raƙuma, to, fa ya zauna a faɗake, ya kintsa sosai.”

  10. Duba, ga wani mutum tafe a keken yaƙin tare da ƙungiyar dawakai. Ya kuma mayar da amsa, ‘Babilon ta fāɗi, ta fāɗi! Dukan siffofin allolinta kwance a ragargaje a ƙasa!’ ”