Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Vanity

88 ayoyi · 60 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. An nuna muku dukan waɗannan abubuwa saboda ku san cewa Ubangiji, shi ne Allah; ban da shi, babu wani.

  2. Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.

  3. Ba na so in zauna da rai; ba zan rayu ba har abada. Ku rabu da ni; rayuwata ba ta da amfani.

  4. Ba shakka yana iya gane mutanen da suke marasa gaskiya; kuma in ya ga abin da yake mugu, ba ya kula ne?

  5. Amma daƙiƙin mutum ba ya taɓa zama mai hikima kamar dai a ce ba a taɓa haihuwar ɗan aholaki horarre.

  6. Kada yă ruɗi kansa ta wurin dogara ga abin da ba shi da amfani domin ba zai samu wani abu ba daga ciki.

  7. Wane ne Maɗaukaki har da za mu bauta masa? Wace riba za mu samu ta wurin yin addu’a gare shi?

  8. Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza?

  9. Har yaushe, ya ku mutane za ku mai da ɗaukakata abin kunya? Har yaushe za ku ƙaunaci ruɗu ku nemi allolin ƙarya? Sela

  10. Bakinsa ya cika da zage-zage da ƙarairayi da kuma barazana; wahala da mugunta suna a ƙarƙashin harshensa.

  11. Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya; zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce suna cike da ruɗu a zukatansu.

  12. Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya, wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.

  13. Ba na zama tare da masu ruɗu, ko in yi tarayya da masu riya;

  14. Na ƙi waɗanda suke manne wa gumakan banza; na dogara ga Ubangiji.

  15. Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta; yakan sa kansa ga aikata zunubi kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau.

  16. Ka sa kwanakina suka zama tafin hannu ne kawai; yawan shekaruna kamar ba kome ba ne a gabanka. Duk ran mutum shaƙar iska ne kurum, har ma waɗanda suke tsammani suke da kāriya. Sela

  17. “Mutum dai shirim ne kawai yayinda yake kai da komowa. Yana ta yawo, amma a banza ne kawai; yakan tara dukiya, ba tare da sanin wa zai more ta ba.

  18. Kakan tsawata ka kuma hore mutane saboda zunubinsu; kakan cinye wadatarsu kamar yadda asu ke yi, kowane mutum dai shaƙar iska ne. Sela

  19. Duk sa’ad da wani ya zo ganina, yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi; sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina.

  20. Ka ba mu gudummawa a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne.

  21. Talakawa dai kamar shaƙar iska suke, Attajirai dai kamar shirim suke; in aka auna a ma’auni, su ba wani abu ba ne; dukansu dai kamar shaƙar iska ne kawai.

  22. Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza shekarunsu kuma cikin masifa.

  23. Ubangiji ya san tunanin mutum; ya san cewa tunaninsu banza ne.

  24. Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani; ka kiyaye raina bisa ga maganarka.

  25. Na ƙi mutane masu baki biyu, amma ina ƙauna dokarka.