Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Vanity: Idolatry is

6 ayoyi · 60 fannoni

Ayoyi game da Idolatry is

  1. Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.

  2. Na ƙi waɗanda suke manne wa gumakan banza; na dogara ga Ubangiji.

  3. Duk masu yin gumaka ba kome ba ne, da kuma abubuwan da suke ɗauka da daraja banza ne. Waɗanda za su yi magana a madadinsu makafi ne; jahilai ne, marasa kunya.

  4. Waɗanda suke siffanta allah su kuma yi zubin gunki, waɗanda ba za su yi musu ribar kome ba?

  5. Dukansu marasa azanci ne wawaye; gumakan itacen banza ne suke koya musu.

  6. Duk da haka mutanena sun manta da ni; sun ƙone turare wa gumaka marasa amfani, waɗanda suka sa su tuntuɓe a al’amuransu a hanyoyin dā. Sun sa suka yi tafiya a ɓarayin hanyoyi a hanyoyin da ba a gina ba.