Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Usury

26 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “In kun ba wa jama’ata matalauta da suke tsakaninku bashin kuɗi, kada ku zama kamar masu ba da rance; kada ku sa yă biya da ruwa.

  2. “ ‘In ɗaya daga ciki mutanen ƙasarku ya talauta, ba ya kuma iya tallafa wa kansa a cikinku, sai ku taimake shi kamar yadda za ku yi da baƙo a cikinku.

  3. Kada ku karɓi riba ta kowace iri daga gare shi, amma ku ji tsoron Allahnku, saboda mutumin ƙasarku yă ci gaba da zama a cikinku.

  4. Kada ku ba shi rancen kuɗi da ruwa, ko ku sayar masa abinci don samun riba.

  5. Kada ku nemi ɗan’uwanku yă biya bashin da kuka ba shi da ruwa, ko kuɗi, ko abinci, ko kowane irin abin da yana iya ba da ruwa.

  6. Za ku iya nemi ruwa a bashin da kuka ba baƙo, amma ba ɗan’uwanku mutumin Isra’ila ba, domin Ubangiji Allahnku yă sa muku albarka a kowane abin da kuka sa hannunku a kai, a ƙasar da kuke shiga ku ci gādonta.

  7. To, sai maza da matansu suka tā da fara gunaguni mai tsanani a kan ’yan’uwansu Yahudawa.

  8. Waɗansu suka ce, “Mu da ’ya’yanmu maza da mata muna da yawa, muna bukatar hatsi domin mu ci mu rayu.”

  9. Waɗansu kuwa suka ce, “Saboda yunwa mun jinginar da gonakinmu, da gonakin inabinmu, da gidajenmu don mu sami hatsi.”

  10. Har illa yau waɗansu suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu.

  11. Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne, ’ya’yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duk da haka an tilasta mu mu sa ’ya’yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma an riga an bautar waɗansu daga cikin ’ya’yanmu mata, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.”

  12. Sa’ad da na ji kukansu da waɗannan koke-koke, na husata ƙwarai.

  13. Na yi tunaninsu a zuciyata sa’an nan na zargi manyan gari da shugabanni. Na ce musu, “Kuna musguna wa ’yan’uwanku ta wurin ba su rance da ruwa!” Saboda haka na kira babban taro gaba ɗaya don a magance wannan.

  14. Na ce, “Da dukan iyakar ƙoƙarinmu, mun fanshi ’yan’uwanmu Yahudawan da aka sayar wa Al’ummai. Amma ga shi kuna sayar da ’yan’uwanku ga Al’ummai, don kawai a sāke sayar mana da su!”

  15. Saboda haka na ci gaba na ce, “Abin da kuke yi a yanzu ba daidai ba ne. Bai kamata ku yi tafiya cikin tsoron Allahnmu don mu guji ba’ar Al’ummai abokan gābanmu ba?

  16. Ni ma da ’yan’uwana da kuma mutanena muna ba wa mutane bashin kuɗi da kuma hatsi. Sai mu daina sha’anin ba da rance da ruwa!

  17. Yau sai ku mayar musu da gonakinsu, da gonakin inabinsu, da na zaitunsu, da gidajensu, da kashi ɗaya bisa ɗari na kuɗi, da na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, waɗanda kuka karɓa a wurinsu.”

  18. Suka ce, “Za mu mayar musu, kuma ba za mu bukaci wani abu daga gare su ba. Za mu yi yadda ka faɗa.” Sai na tattara firistoci na kuma sa manyan gari da shugabanni su yi rantsuwa don su yi abin da suka yi alkawari.

  19. Na kuma kakkaɓe hannuna, na ce, “Duk wanda ya karya wannan alkawari, haka Allah zai kakkaɓe shi daga gidansa da aikinsa. Allah zai kakkaɓe shi, yă wofintar da shi!” Da jin wannan, sai dukan taron suka ce, “Amin,” suka kuma yabi Ubangiji. Mutane kuwa suka yi kamar yadda suka yi alkawari.

  20. wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi. Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa ba zai taɓa jijjiguwa ba.

  21. Duk wanda ya tara dukiyarsa ta wurin ba da bashi da ruwan da ya wuce misali yana tara wa wani ne wanda zai yi wa talakawa alheri.

  22. Kaitona, mahaifiyata, da kika haife ni, mutumin da dukan ƙasa take faɗa take kuma gardama da shi! Ban ba da bashi ko in ci bashi ba, duk da haka kowa yana zagina.

  23. Ba ya ba da bashi da ruwa ko ya karɓa ƙarin riba. Yakan janye hannunsa daga aikata mugunta yakan kuma yi shari’a cikin gaskiya tsakanin mutum da mutum.

  24. Yakan ba da bashi da ruwa ya kuma karɓi riba mai yawa. Irin wannan mutum zai rayu? Ba zai rayu ba! Domin ya aikata dukan waɗannan abubuwa masu banƙyama, tabbatacce za a kashe shi, kuma hakkin jininsa zai zauna a kansa.

  25. Yakan janye hannunsa daga zunubi ba ya kuma ba da bashi da ruwa ko karɓan riba da yawa. Yakan kiyaye dokokina ya kuma bi ƙa’idodina. Ba zai mutu saboda zunubin mahaifinsa ba; tabbatacce zai rayu.