Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Feast of Tabernacles

39 ayoyi · 17 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha.

  2. “ ‘Ban da abin da kuka yi alkawari, da kuma sadakokinku na yardar rai, a miƙa waɗannan ga Ubangiji a lokacin bukukkuwanku, hadayunku na ƙonawa, hadayu na gari, hadayu na sha da hadayu na salama.’ ”

  3. Sa’an nan Musa ya umarce su ya ce, “A ƙarshen kowace shekara bakwai, a shekara ta yafe basusuwa, a lokacin Bikin Tabanakul,

  4. sa’ad da dukan Isra’ila suka zo, don su bayyana a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa, za ku karanta wannan doka a gabansu, a kunnuwansu.

  5. Ku tattara mutane, maza, mata da kuma yara, da baƙin da suke zama a cikin garuruwanku, saboda su saurara, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su lura, su bi dukan kalmomin wannan doka.

  6. Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi; bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.

  7. Ya Ubangiji, ka cece mu; Ya Ubangiji, ka ba mu nasara.

  8. Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji. Daga gidan Ubangiji muna sa muku albarka.

  9. Ubangiji shi ne Allah ya kuma sa haskensa ya haskaka a kanmu. Da kwanoni a hannunmu, muka shiga jerin gwanon biki ku kai su ƙahoni na bagade.

  10. Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya; kai ne Allahna, zan kuwa ɗaukaka ka.

  11. Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

  12. A rana ta ƙarshe kuma mafi girma ta Bikin, Yesu ya tsaya ya yi magana da babbar murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa, yă zo wurina yă sha.

  13. Duk wanda ya gaskata da ni, kamar yadda Nassi ya ce, kogunan ruwa masu rai za su gudana daga cikinsa.”

  14. Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yă zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.