Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Feast of Tabernacles: Singing hosannas
Ayoyi game da Singing hosannas
Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi; bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.
Ya Ubangiji, ka cece mu; Ya Ubangiji, ka ba mu nasara.
Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji. Daga gidan Ubangiji muna sa muku albarka.
Ubangiji shi ne Allah ya kuma sa haskensa ya haskaka a kanmu. Da kwanoni a hannunmu, muka shiga jerin gwanon biki ku kai su ƙahoni na bagade.
Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya; kai ne Allahna, zan kuwa ɗaukaka ka.
Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.