Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Feast of Tabernacles: The law publicly read every seventh year at
Ayoyi game da The law publicly read every seventh year at
Sa’an nan Musa ya umarce su ya ce, “A ƙarshen kowace shekara bakwai, a shekara ta yafe basusuwa, a lokacin Bikin Tabanakul,
sa’ad da dukan Isra’ila suka zo, don su bayyana a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa, za ku karanta wannan doka a gabansu, a kunnuwansu.
Ku tattara mutane, maza, mata da kuma yara, da baƙin da suke zama a cikin garuruwanku, saboda su saurara, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su lura, su bi dukan kalmomin wannan doka.