Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Feast of Tabernacles

39 ayoyi · 17 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A miƙa hadayar da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta bijimai guda sha uku, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

  2. Da kowane bijimai goma sha uku nan, a miƙa hadaya ta gari, kashi uku bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da ragunan biyu ɗin, a miƙa hadaya ta gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai;

  3. tare kuma da kowane ’yan raguna goma sha huɗu, kashi ɗaya bisa goma.

  4. A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa na kullum tare da hadayarta, ta gari da kuma hadaya ta sha.

  5. “ ‘A rana ta biyu, a miƙa bijimai goma sha biyu, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

  6. Tare da bijiman, ragunan da ’yan ragunan a miƙa hadayarsu da gari da hadaya ta sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade.

  7. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya, don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadayunsu ta sha.

  8. “ ‘A rana ta uku za a miƙa bijimai goma sha ɗaya, raguna biyu, da kuma ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

  9. Tare da bijiman, ragunan da ’yan raguna, a miƙa hadayun gari da hadayun sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade.

  10. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.

  11. “ ‘A rana ta huɗu a miƙa bijimai goma, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

  12. Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.

  13. A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.

  14. “ ‘A rana ta biyar a miƙa bijimai tara, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

  15. Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan ragunan, a miƙa hadayu na gari, da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.

  16. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.

  17. “ ‘A rana ta shida a miƙa bijimai takwas, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

  18. Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu ta gari da hadayu na sha bisa adadin da a ƙayyade.

  19. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadaya ta sha.

  20. “ ‘A rana ta bakwai a miƙa bijimai bakwai, raguna biyu da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

  21. Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari, da hadayun sha bisa ga adadin da a ƙayyade.

  22. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha.

  23. “ ‘A rana ta takwas kuwa za a yi tsattsarkan taro, ban da aikin da aka saba.

  24. A miƙa hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, a yi hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.

  25. Tare da bijimin, ragon da kuma ’yan ragunan, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.