Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Altar of Burnt Offering

150 ayoyi · 30 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;

  2. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;

  3. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;

  4. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Abidan ɗan Gideyoni.

  5. A rana ta goma, Ahiyezer ɗan Ammishaddai, shugaban mutanen Dan, ya kawo hadayarsa.

  6. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;

  7. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;

  8. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;

  9. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;

  10. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Ahiyezer ɗan Ammishaddai.

  11. A rana ta goma sha ɗaya, Fagiyel ɗan Okran, shugaban mutanen Asher, ya kawo hadayarsa.

  12. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;

  13. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;

  14. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;

  15. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;

  16. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Fagiyel ɗan Okran.

  17. A rana ta goma sha biyu, Ahira ɗan Enan, shugaban mutanen Naftali, ya kawo hadayarsa.

  18. Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;

  19. kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;

  20. da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;

  21. ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;

  22. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Ahira ɗan Enan.

  23. Waɗannan su ne hadayun shugabannin Isra’ilawa saboda keɓewar bagade sa’ad da aka shafe shi, an kawo faranta goma sha biyu na azurfa, darunan goma sha biyu na azurfa don yayyafawa, da kuma kwanonin zinariya goma sha biyu.

  24. Kowane faranti na azurfa yana da nauyin shekel ɗari da talatin, kuma kowane daro na azurfa don yayyafawa yana da nauyin shekel saba’in. Duka-duka dai, nauyin kwanonin azurfa, shekel dubu biyu ne da ɗari huɗu, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.

  25. Kwanonin zinariya goma sha biyu da aka cika da turaren hayaƙi kuwa, nauyinsu shekel goma ne kowanne, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Duka-duka dai, nauyin kwanonin zinariya, shekel ɗari ɗaya ne da ashirin.