Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Affections

59 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba;

  2. marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta,

  3. Irin su ne suke saɗaɗawa su shiga gidaje suna rinjayar mata marasa ƙarfin hali, waɗanda zunubai suka sha kansu, mugayen sha’awace-sha’awace kuma sun ɗauke hankulansu,

  4. Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci.

  5. Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin sha’awace-sha’awacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki. Da ƙarfin hali da kuma girman kai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama;

  6. Gama suna surutai banza na girman kai, ta wurin son bin fasikanci na mutuntaka, sukan jan hankulan mutanen da suke kuɓucewa daga waɗancan masu zama cikin kuskure.

  7. Duk da haka ina riƙe da wannan game da kai. Ka watsar da ƙaunarka ta farko.

  8. Duk da haka, ina da abubuwa kima game da kai. Kana da mutane a can waɗanda suke riƙe da koyarwar Bala’am, wanda ya koya wa Balak yă ja hankalin Isra’ilawa su yi zunubi ta wurin cin abincin da aka miƙa wa gumaka hadaya, su kuma yi fasikanci.

  9. Duk da haka, ina da wannan game da kai. Kana haƙuri da matan nan Yezebel, wadda take kira kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta tana ɓad da bayina ga yin fasikanci suka kuma ci abincin da aka miƙa wa gumaka.