Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Affections: Upon the house and worship of God

5 ayoyi · 16 fannoni

Ayoyi game da Upon the house and worship of God

  1. Ban da haka ma, cikin sa zuciyata ga haikalin Allahna, yanzu na ba da ma’ajina na zinariya da azurfa saboda haikalin Allahna, fiye da kome na tanada saboda wannan haikali,

  2. Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji, wurin da ɗaukakarka ke zaune.

  3. Abu guda na roƙi Ubangiji, wannan shi ne na nema, cewa in zauna a gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, in dubi kyan Ubangiji in kuma neme shi a cikin haikalinsa.

  4. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Na ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ina misalin kyan wurin zamanka, Ya Ubangiji Maɗaukaki!

  5. Raina yana marmari, har yana suma, don filayen gidan Ubangiji; zuciyata da namana na tā da murya domin Allah mai rai.