Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Samuel

135 ayoyi · 22 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Ubangiji ne ke kawo mutuwa, yă kuma rayar yana kai ga kabari, yă kuma tā da.

  2. Ubangiji ne yakan aika da talauci da kuma dukiya; yakan ƙasƙantar yă kuma ɗaukaka.

  3. Yakan tā da matalauci daga ƙura, yă kuma ɗaga mai bukata daga tarin toka; yă zaunar da su tare da ’ya’yan sarki; yă kuma sa su gāji mulki na ɗaukaka. “Harsashin duniya na Ubangiji ne; a bisansu ne ya kafa duniya.

  4. Zai kiyaye ƙafafun masu tsarki, amma mugaye za su lalace cikin duhu. “Ba bisa ga ƙarfi mutum ba ne mutum ke nasara;

  5. waɗanda suke gāba da Ubangiji za su hallaka. Zai yi musu tsawa daga sama, Ubangiji zai hukunta dukan duniya. “Zai ba wa sarkinsa ƙarfi, yă kuma ɗaukaka shafaffensa.”

  6. Sa’an nan, Elkana ya koma gida a Rama amma yaron ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli firist.

  7. Amma yaron nan Sama’ila, yana hidima a gaban Ubangiji yana sanye da efod na lilin.

  8. Kowace shekara mahaifiyarsa takan ɗinka ’yar taguwa ta kai masa sa’ad da ita da mijinta suka je miƙa hadaya ta shekara.

  9. Hannatu kuwa ta sami alfarma daga Ubangiji. Ta yi ciki. Ana cikin haka Sama’ila kuwa sai girma yake ta yi a gaban Ubangiji.

  10. Yaron nan Sama’ila ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli. A waɗannan kwanaki kuwa jin magana daga wurin Ubangiji ba safai ba, babu kuma wahayi da yawa.

  11. Wata rana da dare Eli da idanunsa sun kusa makancewa har ba ya iya gani sosai yana kwance a inda ya saba.

  12. Fitilar Allah kuwa tana ci, ba tă mutu ba tukuna, Sama’ila kuma na kwance a haikali na Ubangiji inda akwai akwatin Allah.

  13. Sai Ubangiji ya kira Sama’ila. Sama’ila ya amsa ya ce, “Ga ni.”

  14. Sai ya ruga wajen Eli ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Eli ya ce, “Ɗana ban kira ba, je ka kwanta”. Saboda haka ya tafi ya kwanta.

  15. Ubangiji ya sāke kiransa ya ce, “Sama’ila!” Sama’ila ya tashi kuma ya je wurin Eli ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Amma Eli ya ce, “Ban kira ka ba, ɗana koma ka kwanta.”

  16. Sama’ila dai bai riga ya san Ubangiji ba tukuna. Ba a kuma taɓa bayyana maganar Ubangiji a gare shi ba tukuna ba.

  17. Ubangiji ya kira Sama’ila sau na uku, Sama’ila kuma ya tashi ya tafi wurin Eli, “Ga ni, gama ka kira ni.” Sai Eli ya gane cewa Ubangiji ne ke kira yaron.

  18. Saboda haka, Eli ya gaya wa Sama’ila cewa, “Je ka kwanta, in kuma ya kira ka, ka ce masa, ‘Ya Ubangiji ka yi magana gama bawanka yana saurara.’ ” Sama’ila ya koma ya kwanta a wurin kwanciyarsa.

  19. Ubangiji kuma ya zo ya tsaya a wurin, yana kira ya ce, “Sama’ila, Sama’ila!” Kamar yadda ya kira a lokutan baya. Sai Sama’ila ya ce, “Yi magana gama bawanka yana saurara.”

  20. Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Duba ina dab da yin wani abu a Isra’ila da zai sa kunne kowa da yake ji, yă ji tsoro.

  21. A ranar zan cika dukan maganar da na yi game da Eli da iyalinsa, daga farko har ƙarshe.

  22. Gama na gaya masa zan hukunta gidansa har abada saboda zunubin da yake sane da shi; ’ya’yansa sun wulaƙantar da kansu, shi kuma bai tsawata musu ba.

  23. Saboda haka na rantse a kan gidan Eli, ‘Ba za a taɓa shafe laifin gidan Eli da hadaya ko baiko ba.’ ”

  24. Sama’ila kuwa ya kwanta har safe, sa’an nan ya buɗe ƙofofin gidan Ubangiji. Ya ji tsoro yă gaya wa Eli wahayin,

  25. amma Eli ya kira shi ya ce, “Sama’ila, ɗana.” Sama’ila ya ce, “Ga ni.”