Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ruth

48 ayoyi · 8 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Bari Ubangiji yă sāka maka saboda abin da ka yi. Bari Ubangiji, Allah na Isra’ila yă sāka maka a yalwace, a ƙarƙashin fikafikan da ka sami mafaka.”

  2. Ta ce, “Bari in ci gaba da samun tagomashi a idanunka ranka yă daɗe. Ka ta’azantar da ni ka kuma yi wa baranyarka magana mai alheri ko da yake ban kai matsayi ɗaya daga cikin bayinka ’yan mata ba.”

  3. A lokacin cin abinci Bowaz ya ce mata, “Zo nan. Ki ɗebo burodi ki tsoma cikin ruwan inabi.” Da ta zauna tare da masu girbin, sai ya ba ta gasasshe hatsi. Ta ci duk abin da take so har ta bar ragowa.

  4. Da ta tashi don tă yi kala, sai Bowaz ya yi umarni wa samarinsa cewa, “Ko ta tara daga cikin dammuna, kada ku wulaƙanta ta.

  5. Ku kuma riƙa zarar mata waɗansu daga dammunan don ta ɗauka, kada ku kwaɓe ta.”

  6. Saboda haka Rut ta yi kala a gonar har yamma. Sa’an nan ta sussuka hatsin sha’ir da ta kalata ta sami kamar efa.

  7. Wata rana Na’omi surukar Rut ta ce mata, “’Yata, bai kamata in nema miki gida, inda za a tanada miki da kyau?

  8. Bowaz wanda kike aiki da bayinsa ’yan mata ba danginmu ne na kusa ba? Da daren yau zai sussuka sha’ir nasa a masussuka.

  9. Ki yi wanka ki fesa turare, ki kuma sa tufafinki mafi kyau. Sa’an nan ki gangara zuwa masussuka, amma kada ki bari yă san cewa kina a can sai ya gama ci da sha.

  10. Sa’ad da ya kwanta, ki lura da inda yake kwance. Sa’an nan ki tafi ki buɗe ƙafafunsa ki kwanta. Zai faɗa miki abin da za ki yi.”

  11. Rut ta amsa ta ce “Zan yi abin da kika faɗa.”

  12. Saboda haka ta gangara zuwa masussuka ta kuma yi dukan abin da surukarta ta ce ta yi.

  13. Sa’ad da Bowaz ya gama ci da sha yana kuma cikin farin ciki, sai ya tafi ya kwanta a ƙarshen tarin hatsi. Rut kuwa ta sulalle ta je ta buɗe ƙafafunsa ta kwanta.

  14. Da tsakar dare sai wani abu ya firgitar da mutumin, ya kuwa juya sai ya tarar da mace kwance a ƙafafunsa.

  15. Sai ya yi tambaya ya ce, “Ke wace ce?” Ta amsa ta ce, “Ni ce baranyarka Rut, ka rufe ni ta mayafinka da yake kai dangi, mai fansa ne na kusa.”

  16. Ya kuma ce, “Ki kawo gyalenki da kika yafa ki shimfiɗa shi a nan.” Sa’ad da ta yi haka, sai ya zuba mudu shida na sha’ir ya sa mata a kai. Sa’an nan ya koma gari.

  17. Sa’an nan Bowaz ya yi shela wa dattawa da kuma dukan mutane, “A yau ku ne shaidu cewa na saya daga Na’omi dukan mallakar Elimelek, Kiliyon da kuma Malon.

  18. Na kuma ɗauki Rut mutuniyar Mowab, gwauruwar Malon a matsayin matata domin sunan mamaci da kuma mallakarsa yă ci gaba, domin kada sunansa yă ɓace daga cikin iyali ko daga tarihin gari. A yau ku ne shaidu!”

  19. Sai dattawan da kuma dukan waɗanda suke a ƙofar suka ce, “Mu shaidu ne. Bari Ubangiji yă sa macen da take zuwa cikin gidanka ta zama kamar Rahila da Liyatu, waɗanda tare suka gina gidan Isra’ila. Bari ka sami martaba a cikin Efrata ka kuma zama sananne cikin Betlehem.

  20. Ta wurin ’ya’yan da Ubangiji zai ba ka ta wurin wannan mace, bari iyalinka yă zama kamar na Ferez, wanda Tamar ta haifa wa Yahuda.”

  21. Sai Bowaz ya ɗauki Rut ta kuwa zama matarsa. Sa’an nan ya kwana da ita, Ubangiji kuma ya sa ta yi ciki, ta haifi ɗa.

  22. Salmon ya haifi Bowaz, Bowaz ya haifi Obed,

  23. Obed ya haifi Yesse, Yesse kuwa ya haifi Dawuda.