Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Reward

166 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka in kun yi biyayya ga umarnan da nake ba ku a yau cikin aminci, kuna ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna kuma bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku,

  2. sai in aika da ruwan sama a ƙasarku a lokacinsa, ruwan saman bazara da kuma na kaka, don ku tattara hatsinku, sabon inabinku da kuma manku.

  3. Zan tanadar da ciyawa a filaye don shanunku, za ku ci, ku kuma ƙoshi.

  4. Ku yi hankali, kada a ruɗe ku har ku bauta wa alloli, ku kuma yi musu sujada,

  5. Saboda haka, sai ku riƙe waɗannan kalmomina gam a zukatanku da ranku; ku ɗaura su kamar alama a hannuwanku, da goshinku.

  6. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.

  7. Ku rubuta su a kan madogaran ƙofofin gidajenku, da a kan ƙofofinku,

  8. saboda kwanakinku da kwanakin ’ya’yanku su yi tsawo a ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninku, muddin sama tana bisa duniya.

  9. Ga shi, a yau, ina sa a gabanku albarka da kuma la’ana,

  10. albarka in kun yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku, da nake ba ku;

  11. la’ana in ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku, kuka kuma juya daga hanyar da na umarce ku, ta wurin bin waɗansu alloli, waɗanda ba ku sani ba.

  12. Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da za ku shiga ku ci gādonta, sai ku yi shelar albarkun nan a dutsen Gerizim, ku kuma yi na la’ana a dutsen Ebal.

  13. Ku yi hankali kada ku riƙe wannan mugun tunani cewa, “Shekara ta bakwai, shekarar yafewar basusuwa, ta yi kusa,” har ku nuna mugun nufi ga ɗan’uwa mabukaci, ku ƙi ba shi wani abu. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku.

  14. Ku bayar hannu sake gare shi, ku kuma yi haka ba tare da gunaguni ba; saboda wannan fa Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan aikinku, da kuma kome da kuka sa hannunku a kai.

  15. Kullum za ku kasance da matalauta a ƙasar. Saboda haka na umarce ku ku bayar hannu sake ga ’yan’uwa da kuma matalauta, da masu bukata a ƙasarku.

  16. Za ku iya kwashe ’ya’yan, amma ku tabbata kun bar mahaifiyar tă tafi. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai.

  17. Sa’ad da kuke girbi a gonarku, sai kuka manta da dami, kada ku koma don ku ɗauka. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa, saboda Ubangiji Allahnku yă albarkace ku a cikin dukan aikin hannuwanku.

  18. Dole ku kasance da ma’aunin da kuma mudun da yake daidai, kuma na gaskiya, saboda ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.

  19. Sa’ad da kuka haye Urdun, sai waɗannan kabilai su tsaya a bisa Dutsen Gerizim su sa wa jama’a albarka, wato, kabilar Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Yusuf da Benyamin.

  20. Waɗannan kabilai kuma za su tsaya a bisa Dutsen Ebal su furta la’ana, wato, kabilar Ruben, Gad, Asher, Zebulun, Dan da Naftali.

  21. Lawiyawa za su karanta wa dukan mutanen Isra’ila da babbar murya su ce,

  22. “La’ananne ne mutumin da ya sassaƙa siffa, ko ya yi zubin gunki, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannu mai sana’a da aka kafa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  23. “La’ananne ne mutumin da ya ƙasƙantar da mahaifinsa ko mahaifiyarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  24. “La’ananne ne mutumin da ya gusar da dutsen da aka kafa don nuna shaidar iyaka.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”

  25. “La’ananne ne mutumin da ya karkatar da makaho daga hanya.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”