Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Respect of Persons

26 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama Ubangiji Allahnku ne Allahn alloli da Ubangijin iyayengiji, Allah mai girma, mai ƙarfi da kuma mai banrazana, wanda ba ya sonkai, ba ya cin hanci.

  2. Yanzu fa ku ji tsoron Ubangiji. Ku yi hankali a kan abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu ba ya sonkai ko nuna wariya ko cin hanci.”

  3. “In da na danne wa bayina maza da mata hakkinsu, sa’ad da suke da damuwa da ni,

  4. me zan yi lokacin da Allah ya tuhume ni? Me zan ce lokacin da ya tambaye ni?

  5. Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba? Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba?

  6. wanda ba ya nuna sonkai ga ’ya’yan sarki kuma ba ya goyon bayan masu arziki a kan matalauta, gama dukansu shi ya yi su da hannuwansa.

  7. Waɗannan ma maganganun masu hikima ne, Nunan sonkai a shari’a ba shi da kyau.

  8. Nuna sonkai ba shi da kyau, duk da haka mutum zai aikata abin da ba daidai ba saboda ’yar ƙaramar rashawa.

  9. Sa’an nan Bitrus ya fara magana ya ce, “Yanzu na gane yadda gaskiya ne cewa Allah ba ya sonkai

  10. Bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, gama ya tsarkake zukatansu ta wurin bangaskiya.

  11. Gama Allah ba ya nuna bambanci.

  12. Duk waɗanda suka yi zunubi a rashi sanin doka, a rashin doka za su hallaka, waɗanda kuma suka yi zunubi ƙarƙashin doka, a ƙarƙashin doka za a hukunta su.

  13. Gama ba bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa yana kuma ba da albarka a yalwace ga duk masu kira gare shi,

  14. Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne, ko ’yantacce.

  15. Ku kuma masu bayi, dole ku bi da bayinku da kyau. Ku daina ba su tsoro. Ku tuna, ku da su, Maigida ɗaya kuke da shi a sama, kuma ba ya nuna bambanci.

  16. Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai.

  17. ’Yan’uwana, a matsayinmu cikin Ubangiji Yesu Kiristi maɗaukaki, kada ku nuna bambanci.

  18. A ce wani ya shigo cikin taronku saye da zoben zinariya da riguna masu tsada, wani matalauci kuma saye da tsummoki shi ma ya shigo,

  19. in kuka mai da hankali na musamman ga mutumin da yake da riguna masu tsadan nan kuka kuma ce, “Ga wurin zama mai kyau dominka,” amma kuka ce wa matalaucin nan, “Kai tsaya daga can,” ko kuwa, “Ka zauna a ƙasa kusa da ƙafafuna,”

  20. ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ke nan ba, kuka kuma zama alƙalai masu mugayen tunani?

  21. Ku saurara, ’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?

  22. Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu?

  23. Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba?

  24. In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai.

  25. Amma in kuka nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan shari’a kuma ta same ku da laifi a matsayin masu karya doka.