Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Reprobacy

150 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa,

  2. ba ya yiwuwa a sāke kawo su ga tuba in suka kauce, domin suna sāke gicciye Ɗan Allah ke nan suna kuma kunyata shi a gaban jama’a.

  3. Ƙasar da take shan ruwan sama da yake fāɗi a kanta kullum da kuma take ba da hatsin da yake da amfani ga waɗanda ake noma dominsu, takan sami albarkar Allah.

  4. Amma ƙasar da take ba da ƙaya da sarƙaƙƙiya ba ta da amfani tana kuma cikin hatsarin la’ana. A ƙarshe za a ƙone ta.

  5. Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya.

  6. A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za tă cinye abokan gāban Allah.

  7. Duk wanda ya ƙi ya kiyaye dokar Musa akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidar mutum biyu ko uku.

  8. Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri?

  9. Gama mun san shi, wannan wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce; zan rama,” da kuma, “Ubangiji zai yi wa mutanensa hukunci.”

  10. Abu mai matuƙar bantsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai rai.

  11. Ku lura fa kada wani yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai yă tsira har yă kawo rikici, yă kuma ƙazantar da mutane da yawa.

  12. Ku lura kada wani yă zama mai fasikanci, ko marar tsoron Allah kamar Isuwa, wanda saboda ƙwaryar abinci ɗaya tak ya sayar da gādonsa na ɗan fari.

  13. Daga baya, kamar yadda kuka sani, sa’ad da ya nemi yă gāji wannan albarka, aka ƙi shi. Bai sami zarafin tuba ba, ko da yake ya nemi albarkan nan da hawaye.

  14. Kowa ya ga ɗan’uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yă yi masa addu’a. Ta dalilin mai addu’an nan kuwa, Allah zai ba da rai ga mai yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yakan kai ga mutuwa. Ban ce a yi addu’a domin wannan ba.

  15. Na faɗa haka ne domin waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā sun shiga cikinku a ɓoye. Su fa marasa tsoron Allah ne. Su ne waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci, suna kuma mūsun Yesu Kiristi wanda shi ne Makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu.

  16. Ko da yake kun riga kun san duk wannan, ina so in tuna muku cewa Ubangiji ya ceci mutanensa daga Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.

  17. Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan.

  18. Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta.

  19. Haka yake da masu mafarke-mafarken nan, gama sun ƙazantar da jikunansu, suka ƙi bin masu mulki, suna ɓata sunan talikan sararin sama.

  20. Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!”

  21. Duk da haka mutanen nan suna maganar banza a kan kome da ba su gane ba; kuma abubuwan da suka fahimta bisa ga jiki, kamar dabbobi marasa hankali, waɗannan abubuwa ne suke hallaka su.

  22. Kaitonsu! Gama sun kama hanyar Kayinu; sun ruga a guje garin neman riba cikin kuskure kamar Bala’am; aka kuma hallaka su cikin tawayen Kora.

  23. Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus.

  24. Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada.

  25. Duk mai yin laifi yă ci gaba da yin laifi; duk mai aikata ƙazanta yă ci gaba da aikata ƙazanta. Duk mai aikata abin da yake daidai, yă ci gaba da aikata abin da yake daidai. Kuma duk wanda yake mai tsarki, yă ci gaba da yin abin da yake da tsarki.”