Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Proselytes: Were entitled to all privileges

6 ayoyi · 14 fannoni

Ayoyi game da Were entitled to all privileges

  1. “Baƙon da yake zama tare da ku da yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi wa dukan mazan da suke cikin gidansa kaciya; sa’an nan ne zai iya yin abubuwa kamar haifaffen ɗan ƙasa.

  2. Kada baƙon da ya miƙa kansa ga Ubangiji ya ce, “Ai Ubangiji zai ware ni daga mutanensa.” Kada kuma wani bābā ya yi gunaguni cewa, “Ni busasshen itace ne kawai.”

  3. Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Wa bābānnin da suna kiyaye Asabbatai, waɗanda suka zaɓi yin abin da ya gamshe ni suna kuma riƙe da alkawarina kankan,

  4. a gare su cikin haikalina da kuma bangayensa zan ba da matuni da kuma suna mafi kyau fiye da ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata; zan ba su madawwamin sunan da ba za a raba su da shi ba.

  5. Baƙin da suka miƙa kansu ga Ubangiji don su bauta masa, su kuma ƙaunaci sunan Ubangiji, waɗanda kuma suke yin masa sujada, duk waɗanda suka kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba suka kuma riƙe alkawarina kankan,

  6. waɗannan ne zan kai tsattsarkan dutsena in sa su yi farin ciki a gidana na addu’a. Hadayunsu na ƙonawa da sadakokinsu za su zama abin karɓa a bagadena; gama za a ce da gidana gidan addu’a domin dukan al’ummai.”