Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Miraculous Gifts of the Holy Spirit: Foretold
Ayoyi game da Foretold
ku faɗa wa waɗanda suka karai a zukata, “Ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro; Allahnku zai zo, zai zo domin ya ɗau fansa; da ramuwar Allah zai zo don yă cece ku.”
Sa’an nan idanun makafi za su buɗe kunnuwan kurame kuma su ji.
Sa’an nan guragu za su yi tsalle kamar barewa, bebaye kuma su yi sowa don farin ciki. Ruwa zai kwararo daga jeji rafuffuka kuma a cikin hamada.
“Daga baya kuma, zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, tsofaffinku za su yi mafarkai, matasanku za su ga wahayoyi.
Har ma a bisan bayina, maza da mata, zan zuba Ruhuna a kwanakin nan.