Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Mercy

43 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Ga masu aminci, kakan nuna kanka mai aminci, ga marasa laifi, kakan nuna kanka marar laifi,

  2. Da sarkin Isra’ila ya gan su, sai ya tambayi Elisha ya ce, “In kashe su ne, mahaifina? In kashe su?”

  3. Elisha ya ce, “Kada ka kashe su. Za ka kashe mutanen da ka kame da takobi ko bakanka? Ka ba su abinci da ruwa su ci, su sha, sa’an nan su koma wurin maigidansu.”

  4. Saboda haka aka shirya musu babban liyafa, bayan sun ci, suka kuma sha, sai ya tura su zuwa wurin maigidansu. Ta haka ’yan harin Aram suka daina kai hari a yankin Isra’ila.

  5. Ga mai aminci ka nuna kanka mai aminci, ga marar laifi ka nuna kanka marar laifi,

  6. Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa, duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi.

  7. Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba, za a yi wa ’ya’yansu albarka.

  8. Ƙauna da aminci za su sadu; adalci da salama za su yi wa juna sumba.

  9. Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai; ka ɗaura su kewaye da wuyanka, ka rubuta su a allon zuciyarka.

  10. Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau a gaban Allah da kuma a gaban mutane.

  11. Mutumin kirki kan ribance kansa, amma mugu kan kawo wa kansa wahala.

  12. Mai adalci kan kula da bukatun dabbobinsa, amma halaye mafi kyau na mugaye su ne ƙeta.

  13. Duk wanda ya rena maƙwabci ya yi zunubi, amma mai albarka ne wanda yake alheri ga mabukata.

  14. Ba waɗanda suke ƙulla mugunta sukan kauce ba? Amma waɗanda suke ƙulla abin da yake mai kyau sukan sami ƙauna da aminci.

  15. Duk wanda ya zalunci matalauci ya zagi Mahaliccinsu ke nan, amma duk wanda ya yi alheri ga mabukata yana girmama Allah ne.

  16. Ƙauna da aminci kan kiyaye sarki lafiya; ta wurin ƙauna sarautarsa za tă zauna a kafe.

  17. Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna kan sami rai, wadata da girmamawa.

  18. Mai adalci yakan mutu, ba kuwa wanda yakan yi tunani a zuciyarsa; an kwashe mutanen kirki, ba kuwa wanda ya fahimta cewa an kwashe masu adalci don a tsame su daga mugunta.

  19. Saboda haka, ya sarki, ina roƙonka ka karɓi shawarar da zan ba ka; ka furta zunubanka ta wurin yin abin da yake daidai. Ka bar muguntarka, ka aikata alheri ga waɗanda ake wulaƙantawa, wataƙila za a ƙara tsawon kwanakinka da salama.”

  20. Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa, gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar. “Babu aminci, babu ƙauna, babu yarda da Allah a cikin ƙasar.

  21. Saboda wannan ƙasar tana makoki, kuma dukan waɗanda suke zama a cikinta sun lalace; namun jeji da tsuntsayen sararin sama da kuma kifin teku suna mutuwa.

  22. Amma dole ku koma ga Allahnku; ku ci gaba da ƙauna da yin gaskiya, ku kuma saurari Allahnku kullum.

  23. Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau. Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.

  24. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku yi shari’ar gaskiya; ku nuna jinƙai da tausayi ga juna.

  25. Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai, gama za a nuna musu jinƙai.