Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Husband

71 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. sai mahaifin yarinyar da mahaifiyarta su kawo shaida cewa ita budurwa ce wa dattawan gari a ƙofar garin.

  2. Mahaifin yarinyar zai ce wa dattawa, “Na ba da ’yata aure ga wannan mutum, amma ya ƙi ta.

  3. Yanzu ya zage ta cewa, ‘Ban sami ’yarku budurwa ba.’ Amma ga shaidar budurcin ’yata.” Sa’an nan iyayenta za su shimfiɗa zanen a gaban dattawan garin,

  4. dattawan kuwa za su ɗauki mutumin su hukunta shi.

  5. Za su ci masa tara shekel azurfa ɗari, su ba mahaifin yarinyar, domin wannan mutum ya ba wa budurwa mutuniyar Isra’ila mummunan suna. Za tă ci gaba da zama matarsa; ba kuwa zai sake ta ba muddin ransa.

  6. Amma fa in zarge gaskiya ne, ba a kuwa sami shaidar budurcin yarinyar ba,

  7. sai a kawo ta a ƙofar gidan mahaifinta, a can mazan gari za su jajjefe ta da dutse har tă mutu. Ta yi abin kunya a Isra’ila ta wurin lalaci a yayinda take a gidan mahaifinta. Dole ku fid da mugu daga cikinku.

  8. A rana ta bakwai, sa’ad da Sarki Zerzes, ya yi tilis da ruwan inabi, sai ya umarci bābānni bakwai waɗanda suke yin masa hidima, wato, Mehuman, Bizta, Harbona, Bigta, Abagta, Zetar da Karkas,

  9. su kawo Sarauniya Bashti a gabansa, sanye da rawanin sarautarta, don ta nuna kyanta wa mutane da kuma hakimai, gama ita kyakkyawa ce ƙwarai.

  10. Amma da masu hidima suka ba da umarnin sarki, sai Sarauniya Bashti ta ƙi zuwa. Wannan ya ɓata wa sarki rai, ya kuma yi fushi ƙwarai.

  11. Da yake, al’ada ce sarki yă nemi shawara daga sanannu a batun doka da adalci, sai ya yi magana da masu hikima waɗanda suke fahimtar lokuta

  12. suke kuma mafi kusa da sarki. Waɗannan masu hikima kuwa su ne, Karshena, Shetar, Admata, Tarshish, Meres, Marsena da kuma Memukan. Su hakimai bakwai ne na Farisa da Mediya waɗanda suke da dama ta musamman ta kaiwa ga sarki, suke kuma da matsayi mafi girma a masarautar.

  13. Ya ce, “Bisa ga doka, me za a yi wa Sarauniya Bashti? Gama ta ƙi yin biyayya da umarnin sarki Zerzes da bābānni suka kai mata?”

  14. Sai Memukan ya amsa a gaban sarki da hakimai ya ce, “Sarauniya Bashti ta yi laifi, ba ga sarki kaɗai ba, amma ga dukan hakimai ma, da kuma mutanen dukan lardunan sarki Zerzes.

  15. Domin halin Sarauniya zai zama sananne ga dukan mata, ta haka kuwa za su ƙasƙantar da mazansu su kuma ce, ‘Sarki Zerzes ya umarta a kawo Sarauniya Bashti a gabansa, amma ta ƙi zuwa.’

  16. Wannan rana matan hakiman Farisa da na Mediya waɗanda suka ji game da halin sarauniya, za su yi haka wa dukan hakiman sarki. Zai zama babu ƙarshen rashin bangirma da kuma reni.

  17. “Saboda haka, in ya gamshi sarki, bari yă ba da hatimi na sarauta, bari kuma a rubuta shi cikin dokokin Farisa da Mediya, wanda ba za a iya sokewa ba, cewa Bashti ba za tă ƙara zuwa gaban sarkin Zerzes ba. Bari kuma sarki yă ba da matsayinta na sarauta ga wata, wadda ta fi ta.

  18. Ta haka, sa’ad da aka yi shelar dokar sarki ko’ina a fāɗin masarautarsa, dukan mata za su ba wa mazansu girma, daga ƙarami har zuwa babba.”

  19. Sarki da hakimansa suka gamsu da wannan shawara. Saboda haka sarki ya yi kamar yadda Memukan ya faɗa.

  20. Ya aika da saƙo zuwa ga dukan ɓangarorin masarautar, zuwa ga kowane lardi a irin nasa rubutu, zuwa kuma ga kowane mutane a nasu harshe, ana shelar a kowane yare na mutane, cewa kowane mutum yă zama mai mulki bisa gidansa.

  21. Ku sha ruwa daga tankinku, ruwa mai gudu daga rijiyarku.

  22. In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje, rafuffukan ruwanku a dandalin jama’a?

  23. Bari su zama naka kaɗai, don kada ka raba da baƙi.

  24. Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka, bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.

  25. Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani, bari mamanta su ishe ka kullum, bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.