Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Altar: Constructed

4 ayoyi · 11 fannoni

Nemi "Altar"

Ayoyi game da Constructed

  1. Suka yi bagaden ƙona turare da itacen ƙirya. Shi bagaden, murabba’i ne, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu biyu, ƙahoninsa kuwa a haɗe suke da shi.

  2. Suka dalaye saman da dukan gefe-gefen da kuma ƙahonin da zinariya zalla, suka kuma yi zubin zinariya kewaye da shi.

  3. Suka yi zobai biyu na zinariya a ƙarƙashin zubin, biyu-biyu ɗaura da juna, don su riƙe sandunan da za a ɗauka shi.

  4. Suka yi sandunan da itacen ƙirya, suka kuma dalaye su da zinariya.