Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Altar: Mosaic commandments prescribing the construction of

9 ayoyi · 11 fannoni

Ayoyi game da Mosaic commandments prescribing the construction of

  1. “ ‘Ku yi mini bagaden ƙasa, ku kuma miƙa mini hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama, za ku hadayar da tumakinku da awakinku da shanu. Duk inda na sa a girmama sunana, zan zo wurinku, in sa muku albarka.

  2. In kuka yi mini bagade dutse, kada ku gina shi da sassaƙaƙƙun duwatsu, gama inda guduma ta taɓa duwatsun, sun haramtu ke nan.

  3. Kada ku gina wa bagadena matakala, domin kada yayinda wani yana hawa, mutane su ga tsiraicinsa.’

  4. Ku gina bagade wa Ubangiji Allahnku, bagaden dutse. Kada ku yi amfani da wani kayan aiki na ƙarfe a kansu.

  5. Ku gina bagaden Ubangiji Allahnku da duwatsun fili, ku kuma miƙa hadaya ta ƙonawa a kansa ga Ubangiji Allahnku.

  6. Ku miƙa hadayun salama a can, kuna ci, kuna farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku.

  7. Yoshuwa kuwa ya yi wa Ubangiji, Allah na Isra’ila bagade a Dutsen Ebal,

  8. kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarci Isra’ilawa. Ya gina bisa ga abin da yake a rubuce a cikin Littafin Dokoki na Musa, bagade na duwatsun da ba a sassaƙa su ba, waɗanda ba wani ƙarfen da ya taɓa su. Suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa da hadayu na salama a kai.

  9. “Waɗannan su ne aune-aunen bagade a tsawon kamu, wannan kamu shi ne kamun tafin hannu. Zurfin magudanar ruwansa kamu ɗaya ne fāɗinsa kuma kamu ɗaya, tare da da’ira kamun tafi ɗaya kewaye da gefensa. Wannan kuma shi ne tsayin bagaden.