- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Abed-Nego
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Daga cikin waɗannan da aka zaɓa akwai waɗansu daga Yahuda, Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya.
Sai sarkin fada ya raɗa musu sababbin sunaye, ga Daniyel ya raɗa masa Belteshazar; ga Hananiya ya raɗa masa Shadrak; ga Mishayel ya raɗa masa Meshak; ga Azariya kuma ya raɗa masa Abednego.
Amma Daniyel ya ƙudura a zuciyarsa ba zai ƙazantar da kansa da abinci da ruwan inabin sarki ba, sai ya tambayi sarkin fada don a ba shi izinin kada yă ƙazantar da kansa ta wannan hanya.
Sai Allah ya sa sarkin fada ya nuna masa tagomashi ya kuma ƙaunaci Daniyel,
amma sai sarkin fada ya ce wa Daniyel, “Ina jin tsoron ranka yă daɗe, sarkina wanda ya sa a ba ku abinci da ruwan inabi. Me zai sa yă ga kuna ramewa fiye da sauran samari, tsaranku? Sarki zai sa a fille mini kai saboda ku.”
Sai Daniyel ya ce wa mai gadi wanda sarkin fada ya sa yă kula da Daniyel, Hananiya, Mishayel da Azariya,
“Ina roƙonka ka gwada bayinka kwana goma. Kada ka ba mu kome sai kayan lambu mu ci da kuma baƙin ruwa mu sha.
Sa’an nan sai ka dubi fuskokinmu da na sauran samarin da suke ci daga abincin sarki; sa’an nan ka yi da bayinka bisa ga abin da ka gani.”
Sai ya amince da haka ya kuma gwada su har kwana goma.
A ƙarshen kwana goma sai aka ga fuskokinsu suna sheƙi, sun kuma yi ƙiba fiye da samarin da suke cin abinci irin na sarki.
Sai mai gadinsu ya janye abinci da ruwan inabi irin na sarki, ya ci gaba da ba su kayan lambu.
Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki.
A ƙarshen lokacin da sarki ya sa da za a kawo su ciki, sai sarkin fada ya gabatar da su ga Nebukadnezzar.
Sarki kuwa ya yi magana da su, sai ya gano cewa babu wani kamar Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya; don haka sai suka shiga yi wa sarki hidima.
A dukan al’amuran hikima da na fahimta wanda sarki ya tambaye su, ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa sau goma.
Sa’an nan Daniyel ya komo gida ya kuma sanar wa abokansa Hananiya, Mishayel da Azariya, batun nan duka.
Bugu da ƙari, bisa ga bukatar Daniyel sai sarki yă naɗa Shadrak da Meshak da Abednego su zama masu kula da harkokin lardin Babilon, amma Daniyel kuma ya tsaya a fadar sarki.
Amma sai ga waɗansu Yahudawa waɗanda ka ɗora su a kan harkokin yankin Babilon, wato, Shadrak, Meshak da Abednego waɗanda ba su kula da umarninka ba, ya sarki. Ba su bauta wa allolin ba balle su yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa.”
Cikin fushi da hasala, Nebukadnezzar ya aika a kira Shadrak, Meshak da Abednego. Aka kawo waɗannan mutane a gaban sarki,
sai Nebukadnezzar ya ce musu, “Gaskiya ne Shadrak, Meshak da Abednego, cewa kun ƙi ku bauta wa alloli kuka kuma ƙi yi sujada ga gunkin da na kafa?
Yanzu sa’ad da kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, in kuna a shirye ku rusuna ƙasa ku yi wa wannan gunkin da na yi sujada, to, da kyau. Amma in ba ku yi sujada ba, za a je fa ku yanzu a cikin tanderun wutar nan. In ga kowane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”
Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka amsa wa sarki suka ce, “Ya Nebukadnezzar, ba mu bukata mu kāre kanmu a gabanka a kan wannan batu.
In an jefa mu cikin tanderun wutar nan, Allahn da muke bauta wa zai iya cetonmu daga ita, kuma ya sarki, zai cece mu daga hannunka.
Amma ko da bai cece mu ba, muna so ka sani, ya sarki; cewa ba za mu bauta wa allolinka ba ko kuma mu yi sujada ga gunkin zinariyar da ka kafa ba.”
Sai Nebukadnezzar ya husata da Shadrak, Meshak da Abednego, sai al’amuransa a kansu ya canja. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar har sau bakwai domin tă yi zafi fiye da yadda take a dā.