Tsallake zuwa abun ciki

Sodom

47 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Sodoma

31.1900, 35.3900 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Sodom

Tace bisa littafi
  1. Babilon, kayan daraja na mulkoki, abin fariyar Babiloniyawa, Allah zai kaɓantar da ita kamar yadda ya yi da Sodom da Gomorra.

  2. A cikin annabawan Urushalima kuma na ga wani abin bantsoro. Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya. Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta, domin kada wani ya juya daga muguntarsa. Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni; mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.”

  3. Kamar yadda aka tumɓuke Sodom da Gomorra, tare da garuruwan da suke maƙwabtaka da su,” in ji Ubangiji, “haka ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta.

  4. Yadda Allah ya tumɓuke Sodom da Gomorra tare da maƙwabtan garuruwansu,” in ji Ubangiji “haka ma ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta.

  5. Horon mutanena ya fi na Sodom girma, wadda aka hallaka farat ɗaya ba wani hannu da ya juya ya taimake ta.

  6. Babbar ’yar’uwarki mutuniyar Samariya ce, wadda take zaune da ’ya’yanta mata wajen arewa da ke; ƙanuwarki ita ce Sodom wadda take zaune kudu da ke tare da ’ya’yanta mata.

  7. Muddin in raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ’yar’uwarki Sodom da ’ya’yanta mata ba su yi abin da ’ya’yanki mata suka yi ba.

  8. “ ‘To, fa, ga zunubin ’yar’uwarki Sodom. Ita da ’ya’yanta mata sun yi girman kai, sun ƙoshi fiye da kima kuma ba su kula da wani abu ba; ba su taimaki matalauta da kuma masu bukata ba.

  9. “ ‘Amma fa, zan komo da nasarar Sodom da ’ya’yanta mata da ta Samariya da ’ya’yanta mata, nasararki kuma tare da su,

  10. ’Yan’uwanki kuwa, Sodom da ’ya’yanta mata da Samariya tare da ’ya’yanta mata, za su koma kamar yadda suke a dā; ke kuma da ’ya’yanki mata za ku koma kamar yadda kike a dā.

  11. Ba za ki ma iya ambaci ’yar’uwarki Sodom a ranar fariyarki ba,

  12. “Na hallaka waɗansunku kamar yadda na hallaka Sodom da Gomorra. Kuna kama da itace mai cin wutar da na cire daga cikin wuta, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.

  13. Saboda haka, muddin ina raye,” in ji Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, “tabbatacce Mowab za tă zama kamar Sodom, Ammonawa kuma kamar Gomorra, ƙasa mai ciyayi da rammukan gishiri, ƙasa marar amfani har abada. Raguwar mutanena za su washe su; waɗanda suka rage na al’ummata za su gāda ƙasarsu.”

  14. Gaskiya nake gaya muku, za a fi jin tausayin Sodom da Gomorra a ranar shari’a fiye da wannan gari.

  15. Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaga ki sama ne? A’a, za ki gangara zuwa zurfafa ne. Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne a aka yi a Sodom, da tana nan har yă zuwa yau.

  16. Amma ina gaya miki, za a fi jin tausayin Sodom fiye da ke a ranar shari’a.”

  17. Ina dai faɗa muku, a ranan nan, za a fi jin tausayin Sodom fiye da wannan garin.

  18. Amma a ranar da Lot ya bar Sodom, sai aka yi ruwan wuta da farar wuta daga sama, aka hallaka su duka.

  19. Yana nan kamar yadda Ishaya ya riga ya faɗa. “Da ba don Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana zuriya ba, da mun zama kamar Sodom, da mun kuma zama kamar Gomorra.”

  20. in har ya hukunta biranen Sodom da Gomorra ta wurin ƙone su suka zama toka, ya kuma maishe su misali na abin da zai faru da marasa tsoron Allah;

  21. Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta.

  22. Gawawwakinsu za su kasance a kwance a titin babban birni, wanda a misalce ake kira Sodom da Masar, inda kuma aka gicciye Ubangijinsu.