Tsallake zuwa abun ciki

Egypt

561 verses · 4 known names

An kuma san shi da: Egyptian, Egyptians, Egyptian's

30.1000, 31.3300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Egypt

Tace bisa littafi
  1. “Allah ya fitar da su daga Masar; suna da ƙarfin kutunkun ɓauna. Sun cinye abokan gāban, suka kakkarya ƙasusuwansu; da kibiyoyinsu suka sossoke su.

  2. “Ku ƙidaya maza daga mai shekara ashirin zuwa gaba yadda Ubangiji ya umarci Musa.” Waɗannan su ne Isra’ilawan da suka fito daga Masar.

  3. sunan matan Amram shi ne Yokebed, ita zuriyar Lawi ce, wadda aka haifa wa Lawiyawa a Masar. A wajen Amram kuwa ta haifi Haruna, Musa da kuma ’yar’uwarsu Miriyam.

  4. ‘Tabbatacce ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba, da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, domin ba su bi ni sosai ba,

  5. Ga wuraren da Isra’ilawa suka yi sansani sa’ad da suka fito runduna-runduna a ƙarƙashin Musa da Haruna daga Masar.

  6. Bisa ga umarni Ubangiji, Haruna firist, ya hau Dutsen Hor, inda ya mutu a rana ta fari ga watan biyar, a shekara ta arba’in, bayan Isra’ilawa suka fito daga Masar.

  7. Kuka yi gunaguni a cikin tentunanku, kuna cewa, “Ubangiji ya ƙi mu; shi ya sa ya fitar da mu daga Masar don yă ba da mu ga hannuwan Amoriyawa su hallaka mu.

  8. Ubangiji Allahnku yana a gabanku, zai yi yaƙi saboda ku, kamar yadda ya yi a kan idanunku a Masar,

  9. Amma ku, Ubangiji ya ɗauke ku, ya fid da ku daga matuya mai narken ƙarfe, wato, daga Masar, domin ku zama jama’arsa ta musamman kamar yadda kuke a yau.

  10. Akwai wani allahn da ya taɓa yin ƙoƙari yă ɗauko wa kansa wata al’umma daga wata al’umma, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu masu banmamaki da al’ajabai, ta wurin yaƙi, ta wurin hannu mai iko, da kuma hannu mai ƙarfi, ko kuwa ta wurin ayyuka masu bangirma da na banmamaki, kamar dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi saboda ku a Masar, a kan idanunku?

  11. Domin ya ƙaunaci kakanninku, ya kuma zaɓi zuriyarsu a bayansu, ya fitar da ku daga Masar ta wurin kasancewarsa da kuma ƙarfinsa mai girma,

  12. Waɗannan su ne farillai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Musa ya ba su, sa’ad da suka fito daga Masar.

  13. Sa’ad da suke a kwari kusa da Bet-Feyor, gabas da Urdun, a ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon, da Musa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi sa’ad da suka fito daga Masar.

  14. “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta.

  15. Ka tuna fa, dā kai bawa ne a ƙasar Masar amma Ubangiji Allahnka ya fitar da kai daga can da iko da kuma ƙarfi. Saboda haka Ubangiji Allahnka ya umarce ka ka kiyaye ranar Asabbaci.

  16. ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar, da gidan bauta ba.

  17. Sai ku gaya musu, “Dā mu bayin Fir’auna ne a Masar, amma Ubangiji ya fitar da mu daga Masar da hannu masu ƙarfi.

  18. A idanunmu Ubangiji ya aikata manyan alamu masu banmamaki, da al’ajabai gāba da Masarawa, da Fir’auna, da kuma dukan gidansa.

  19. Amma ya zama haka domin Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma kiyaye rantsuwar da ya yi wa kakanninku da ya fitar da ku da hannu mai ƙarfi, ya kuma cece ku daga ƙasar bauta, daga ikon Fir’auna sarkin Masar.

  20. Ubangiji zai kiyaye ku daga kowace cuta. Ba zai wahalshe ku da mugayen cututtukan da kuka sani a Masar ba, amma zai aukar wa dukan maƙiyanku.

  21. Amma kada ku ji tsoronsu; ku tuna da kyau abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Fir’auna da kuma dukan Masar.

  22. to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma.

  23. Ku tuna da wannan, kada kuma ku manta yadda kuka tsokane Ubangiji Allahnku, har ya yi fushi a hamada. Daga ranar da kuka bar Masar har sai da kuka isa nan, kuna ta tawaye wa Ubangiji.

  24. Sa’an nan Ubangiji ya faɗa mini, “Sauka daga nan da sauri, domin mutanenka waɗanda ka fitar da su daga Masar sun lalace. Sun juye da sauri daga abin da na umarce su, suka kuma yi zubin gunki wa kansu.”

  25. Na yi addu’a ga Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kada ka hallaka mutanenka, gādon kanka, da ka fansa ta wurin ikonka mai girma, ka kuma fitar da su daga Masar da hannu mai ƙarfi.