Jesus
An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ
Ayoyin da suka ambaci Jesus
Ya kuma ba shi iko yă hukunta domin shi Ɗan Mutum ne.
“Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa
Ni kaɗai dai ba na iya yin kome, ina shari’a ne bisa ga abin da na ji. Shari’ata kuwa mai adalci ce. Gama ba na neman gamsar da kaina, sai dai in gamshi shi wanda ya aiko ni.
“In na ba da shaida a kaina, shaidata ba gaskiya ba ce.
Akwai wani mai ba da shaida mai kyau a kaina, na kuma san cewa shaidarsa game da ni gaskiya ce.
Ba cewa ina neman shaidar mutum ba ne; sai dai na faɗi haka ne domin ku sami ceto.
“Ina da shaidar da ta fi ta Yohanna ƙarfi. Gama aikin nan da Uba ya ba ni in kammala, wanda kuwa nake yi, yana ba da shaida cewa Uba ne ya aiko ni.
Uba da ya aiko ni kuwa kansa ya yi shaida game da ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ko ganin siffarsa ba,
maganarsa kuwa ba ta zama a cikinku, gama ba ku gaskata da wanda ya aiko ni ba.
Kuna ta nazarin Nassosi da himma don kuna tsammani ta wurinsu ne kuna samun rai madawwami. Nassosin nan ne suke ba da shaida a kaina,
duk da haka kun ƙi zuwa wurina domin ku sami rai.
“Ni ba na neman yabon mutane,
na fa san ku. Na san cewa ba ku da ƙaunar Allah a cikin zukatanku.
Na zo a cikin sunan Ubana, ba ku kuwa karɓe ni ba; amma a ce wani dabam ya zo a cikin sunan kansa, za ku karɓe shi.
“Kada fa ku yi tsammani zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi.
Da a ce kun gaskata da Musa, da kun gaskata ni, domin ya rubuta game da ni.
Amma da yake ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, yaya za ku gaskata maganata?”
Ɗan lokaci bayan wannan, sai Yesu ya ƙetare zuwa gaɓar mai nesa na Tekun Galili (wato, Tekun Tibariya),
sai taro mai yawa na mutane suka bi shi domin sun ga abubuwan banmamakin da ya yi ga marasa lafiya.
Sa’an nan Yesu ya hau gefen dutse ya zauna tare da almajiransa.
Sa’ad da Yesu ya ɗaga kai ya ga taro mai yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayi burodi saboda mutanen nan su ci?”
Ya yi wannan tambayar don yă gwada shi ne kawai, gama ya riga ya san abin da zai yi.
Sai Filibus ya amsa ya ce, “Kai, ko albashin wata takwas ba zai iya sayan isashen burodin da kowa zai ɗan samu kaɗan ba!”
Sai wani daga cikin almajiransa Andarawus, ɗan’uwan Bitrus, ya yi magana,
Yesu ya ce, “Ku sa mutanen su zauna.” Wurin kuwa akwai ciyawa da sosai, sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar.