God
Ayoyin da suka ambaci God
Wata rana na tafi gidan Shemahiya ɗan Delahiya, ɗan Mehetabel, wanda aka hana fita a gidansa. Ya ce mini, “Mu sadu gobe a gidan Allah, a cikin haikali, mu kuma kulle ƙofofin haikali, gama mutane suna zuwa su kashe ka, tabbatacce za su zo da dare su kashe ka.”
Na gane cewa Allah bai aike shi ba, ya yi annabci a kaina domin Tobiya da Sanballat sun yi hayarsa ne.
Ya Allahna, ka tuna da Tobiya da Sanballat, saboda abin da suka yi; ka kuma tuna da annabiya Nowadiya da sauran annabawa waɗanda suke ƙoƙari su tsorata ni.
Sa’ad da dukan abokan gābanmu suka ji haka, dukan al’umman da suke kewaye da mu suka ji tsoro, suka rasa ƙarfin halinsu, domin sun gane cewa wannan aiki an yi shi da taimakon Allahnmu ne.
Na sa ɗan’uwana Hanani tare da Hananiya shugaban fada aikin riƙon Urushalima, domin shi Hananiya mutum mai mutunci ne, mai tsoron Allah fiye da yawancin mutane.
Sai Allahna ya sa a zuciyata in tara manyan gari, shugabanni da talakawa don a rubuta su bisa ga iyalansu. Na sami littafin asali na waɗanda suka fara dawowa. Ga abin da na tarar an rubuta a ciki.
sai dukan mutane suka taru kamar mutum guda a dandali a gaban Ƙofar Ruwa. Suka faɗa wa Ezra malamin Doka yă fitar da Littafin Dokar Musa, wanda Ubangiji ya umarta domin Isra’ila.
Ezra ya yabi Ubangiji, Allah mai girma; dukan mutane kuwa suka tā da hannuwansu suka amsa, “Amin! Amin!” Sa’an nan suka sunkuya suka yi wa Ubangiji sujada da fuskokinsu har ƙasa.
Suka karanta daga Littafin Dokar Allah, suna sa kowa ya gane, suna kuma ba da fassarar domin mutane su fahimci abin da ake karatu.
Sa’an nan Nehemiya gwamna, Ezra firist da kuma wanda yake malamin Doka, da Lawiyawa waɗanda suke koyar da mutane, suka ce musu duka, “Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangiji Allahnku. Kada ku yi makoki ko kuka.” Gama dukan mutane suna ta kuka yayinda suke sauraran kalmomin Dokar.
Nehemiya ya ce, “Ku koma gidajenku ku ci abinci mai kyau, ku sha abin sha mai zaƙi, ku kuma aika wa wanda ba shi da shi. Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangijinmu. Kada ku yi baƙin ciki, gama farin cikin Ubangiji shi ne ƙarfinku.”
Suka tarar a rubuce a cikin Doka wadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa, cewa Isra’ilawa su zauna a bukkoki a lokaci bikin watan bakwai
Sai mutanen suka fita suka dawo da rassa suka kuma yi wa kansu bukkoki a bisa rufin ɗakunansu, a cikin filaye, a shirayin gidan Allah, da ciki dandalin da yake kusa da Ƙofar Ruwa, da kuma a dandalin da yake a Ƙofar Efraim.
Kowace rana, daga rana farko zuwa ƙarshe, Ezra ya karanta daga Littafin Dokar Allah. Suka yi bikin kwana bakwai, a rana ta takwas kuma suka yi muhimmin taro bisa ga ƙa’ida.
Sa’ad da suke nan a tsaye, aka ɗauki awa uku ana karanta Littafin Dokar Ubangiji Allahnsu. Aka kuma ɗauki awa uku ana sujada ga Ubangiji Allahnsu.
A kan dakalin kuwa akwai Lawiyawa, wato, Yeshuwa, Bani, Kadmiyel, Shebaniya, Bunni, Sherebiya, Bani da Kenani tsaye, waɗanda suka kira da babbar murya ga Ubangiji Allahnsu.
Lawiyawan nan, Yeshuwa, Kadmiyel, Bani, Hashabnehiya, Sherebiya, Hodiya, Shebaniya da Fetahahiya, suka ce, “Ku miƙe tsaye ku yabi Ubangiji Allahnku, wanda yake har abada abadin.” “Albarka ta tabbata ga sunanka mai ɗaukaka, bari kuma a ɗaukaka shi bisa dukan albarka da yabo.
Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.
“Kai ne Ubangiji Allah, wanda ya zaɓi Abram, ya fitar da shi daga Ur na Kaldiyawa, ya kuma ba shi suna Ibrahim.
Kai ka sami zuciyarsa da aminci a gare ka, ka kuma yi alkawari da shi cewa za ka ba zuriyarsa ƙasar Kan’aniyawa, da ta Hittiyawa, da ta Amoriyawa, da ta Ferizziyawa, da ta Yebusiyawa, da kuma ta Girgashiyawa. Ka kiyaye alkawarinka domin kai mai adalci ne.
Ka aika da alamu masu banmamaki da al’ajabai a kan Fir’auna, a kan dukan shugabanninsa da kuma a kan dukan mutanen ƙasarsa, gama ka ga irin danniyar da suka yi wa mutanenka. Ka samo wa kanka suna, wadda ta dawwama har yă zuwa yau.
Ka raba teku a gaban kakanninmu, saboda su wuce cikinsa a busasshiyar ƙasa, amma ka hallaka masu binsu cikin zurfafa, nutse kamar dutse a cikin ruwa.
Da rana ka bishe kakanninmu da girgije, da dare kuwa ka bishe su da ginshiƙin wuta don ka ba su haske a hanyar da za su bi.
Ka sanar da su Asabbacinka mai tsarki, ka kuma ba su umarnai, da farillai, da kuma dokoki ta wurin bawanka Musa.
Cikin yunwansu ka ba su burodi daga sama, cikin ƙishirwansu kuma ka fitar musu ruwa daga dutse. Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka rantse ta wurin ɗaga hannu cewa za ka ba su.