Nehemiya 11:20-36
20
Sauran Isra’ilawa tare da firistoci, da Lawiyawa sun kasance a dukan garuruwan Yahuda, kowanne a mallakar kakansa.
21
Ma’aikatan haikali sun zauna a kan tudun Ofel. Ziha, da Gishfa ne suke lura da su.
22
Babban shugaban Lawiyawa a Urushalima shi ne Uzzi ɗan Bani, ɗan Hashabiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mika. Uzzi yana ɗaya daga zuriyar Asaf, waɗanda suke mawaƙan da suke da nawayar hidima a gidan Allah.
23
Mawaƙa sun bi umarnan sarki, a kan abin da za su yi kowace rana.
24
Fetahahiya ɗan Meshezabel, ɗaya daga zuriyar Zera ɗan Yahuda ne, wakilin sarki cikin dukan al’amuran da suka shafi mutane.
25
Game da ƙauyukan da filayensu, waɗansu mutanen Yahuda suka zauna a Kiriyat Arba da ƙauyukanta, da Dibon da ƙauyukanta, da Yekabzeyel da ƙauyukanta.
26
Akwai su kuma a Yeshuwa, da Molada, da Bet-Felet,
27
da Hazar Shuwal, da Beyersheba da ƙauyukanta.
28
Akwai su a Ziklag, da Mekona da ƙauyukanta.
29
Suna nan kuma a En Rimmon, da Zora, da Yarmut,
30
da Zanowa, da Adullam da ƙauyukansu, da Lakish da gonakinta, da kuma Azeka da ƙauyukanta. Saboda haka sun yi zama tun daga Beyersheba har zuwa Kwarin Hinnom.
31
Zuriyar mutanen Benyamin daga Geba sun zauna a Mikmash, da Aiya, da Betel da ƙauyukanta,
32
da Anatot, da Nob, da Ananiya,
33
da Hazor, da Rama, da Gittayim,
34
da Hadid, da Zeboyim, da Neballat,
35
da Lod, da Ono, da kuma a Kwarin Masu sana’a.
36
Waɗansu gundumomin Lawiyawan Yahuda sun zauna a Benyamin.
Settings