Nehemiya 11:15-19
15
Daga Lawiyawa kuwa akwai, Shemahiya ɗan Hasshub, ɗan Azrikam, ɗan Hashabiya, ɗan Bunni,
16
da Shabbetai, da kuma Yozabad, biyu cikin shugabanni Lawiyawa waɗanda suke da nawayar aiki waje da gidan Allah.
17
Sai kuma Mattaniya ɗan Mika, ɗan Zabdi, ɗan Asaf, shugaban da yake bi da hidimar godiya da kuma addu’a. Sai Bakbukiya, na biyu a cikin ’yan’uwansa; da Abda ɗan Shammuwa, ɗan Galal, ɗan Yedutun.
18
Lawiyawan da suke cikin birni mai tsarki sun kai 284.
19
Matsaran ƙofofi kuwa su ne, Akkub, da Talmon, da ’yan’uwansu waɗanda suke tsaron ƙofofi, su 172 ne.
Settings