Nehemiya 11:10-14
10
Daga firistoci akwai, Yedahiya ɗan Yohiyarib, da Yakin,
11
da Serahiya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, mai lura da abubuwa a cikin gidan Allah,
12
tare da ’yan’uwansu waɗanda suke aiki domin haikali, su 822 ne. Akwai kuma Adahiya ɗan Yeroham, ɗan Felaliya, ɗan Amzi, ɗan Zakariya, ɗan Fashhur, ɗan Malkiya,
13
da ’yan’uwansa waɗanda suke shugabannin iyalai, su 242. Sai kuma Amashsai ɗan Azarel, ɗan Ahzai, ɗan Meshillemot, ɗan Immer,
14
da ’yan’uwansa, su 128 ne muhimman mutane. Babban shugabansu shi ne Zabdiyel ɗan Haggedolim.
Settings