Skip to content
Nehemiya 11:3-9

Nehemiya 11:3-9

3
Waɗannan su ne shugabannin yankuna waɗanda suka zauna a Urushalima (ko da yake waɗansu Isra’ilawa, da firistoci, da Lawiyawa, da ma’aikatan haikali, da zuriyar bayin Solomon, suka yi zama a cikin garuruwan Yahuda, kowanne a mallakarsa cikin garuruwa dabam-dabam,
4
yayinda sauran mutane daga Yahuda da Benyamin suka zauna a Urushalima). Daga zuriyar Yahuda akwai, Atahiya ɗan Uzziya, ɗan Zakariya, ɗan Amariya, ɗan Shefatiya, ɗan Mahalalel, wani zuriyar Ferez;
5
da Ma’asehiya ɗan Baruk, ɗan Kol-Hoze, ɗan Hazahiya, ɗan Adahiya, ɗan Yohiyarib, ɗan Zakariya, zuriyar Shela.
6
Zuriyar Ferez waɗanda suka zauna a Urushalima sun kai ɗari huɗu da sittin da takwas, dukansu kuwa muhimman mutane ne.
7
Daga zuriyar Benyamin akwai, Sallu ɗan Meshullam, ɗan Yowed, ɗan Fedahiya, ɗan Kolahiya, ɗan Ma’asehiya, ɗan Itiyel, ɗan Yeshahiya,
8
da mabiyansa, Gabbai da Sallai, mutum 928.
9
Yowel ɗan Zikri ne babban shugabansu, Yahuda kuma ɗan Hassenuwa, ya shugabanci Yanki na Biyu na birni.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options