Mattiyu 24:4-28
4
Yesu ya amsa, “Ku lura fa, kada wani yă ruɗe ku.
5
Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kiristi,’ za su kuwa ruɗi mutane da yawa.
6
Za ku ji labarin yaƙe-yaƙe da kuma jita-jitarsu, sai dai ku lura kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru, amma ƙarshen tukuna.
7
Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki yă tasar wa mulki. Za a yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam.
8
Dukan waɗannan fa, mafarin azabar naƙudar haihuwa ne.
9
“Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni.
10
A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,
11
annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.
12
Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za tă yi sanyi,
13
amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.
14
Za a kuma yi wa’azin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yă zama shaida ga dukan al’ummai, sa’an nan ƙarshen yă zo.
15
“Saboda haka sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a tsattsarkan wuri (mai karatu yă gane),
16
to, sai waɗanda suke cikin Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu.
17
Kada wani da yake a kan rufin gidansa, yă sauko don ɗaukar wani abu a gida.
18
Kada wani da yake gona kuma yă komo don ɗaukar rigarsa.
19
Kaiton mata masu ciki da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin!
20
Ku yi addu’a, kada gudunku yă zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci.
21
Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba.
22
“Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin.
23
A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata.
24
Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.
25
Ga shi, na faɗa muku tun da wuri.
26
“Saboda haka in wani ya ce muku, ‘Ga shi can a hamada,’ kada ku fita; ko, ‘Ga shi nan a ɗakunan ciki,’ kada ku gaskata.
27
Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance.
28
Duk inda mushe yake, can ungulai za su taru.
Settings