Mahukunta 18:1-16
1
To, a kwanakin nan Isra’ila ba ta da sarki. A kwanakin kuwa zuriyar Dan tana neman wurinsu na zama, gama ba su riga sun sami gādo tare da kabilan Isra’ila ba.
2
Saboda haka mutanen Dan suka aika jarumawa guda biyar daga Zora da Eshtawol don su leƙi asirin ƙasar su kuma bincike ta. Waɗannan mutanen sun wakilci dukan kabilar. Suka ce musu, “Ku je, ku bincike ƙasar.” Mutanen suka shiga ƙasar tudu ta Efraim suka zo gidan Mika, inda suka kwana.
3
Sa’ad da suka yi kusa da gidan Mika, sai suka gane muryar saurayin nan Balawe; saboda haka suka shiga wurin suka tambaye shi, “Wa ya kawo ka nan? Me kake yi a nan? Me ya sa kake a nan?”
4
Ya gaya musu abin da Mika ya faɗa masa ya ce, “Ya ɗauke ni aiki ya kuma sa in zama masa firist.”
5
Sa’an nan suka ce masa, “Muna roƙonka ka nemi mana nufin Allah don mu sani ko tafiyarmu tana da nasara.”
6
Firist ya amsa ya ce, “Ku sauka lafiya, gama tafiyarku tana da yardan Ubangiji.”
7
Saboda haka mutum biyar ɗin suka tashi suka iso Layish, inda suka ga mutane suna zamansu a huce, kamar Sidoniyawa, ba sa zato ga tsaro. Kuma da yake ƙasarsu ba ta bukata kome, suna da wadata. Suna kuma nesa da Sidoniyawa, ba sa kuma hulɗa da kowa.
8
Da suka komo Zora da Eshtawol, ’yan’uwansu suka tambaye su, “Me kuka gano?”
9
Suka ce, “Ku zo mu yaƙe su! Mun ga ƙasar tana da kyau sosai. Ba za ku yi wani abu ba? Kada ku yi wata-wata, ku je kun mallaki ƙasar.
10
Sa’ad da kun kai can, za ku iske mutanen suna zama a sake, ƙasar kuwa mai faɗi ce wadda Allah ya sa a hannuwanku, ƙasar da ba tă rasa kome ba.”
11
Sai mutane ɗari shida daga kabilar Dan suka yi ɗamarar yaƙi, suka tashi daga Zora da Eshtawol.
12
A kan hanyarsu suka kafa sansani kusa da Kiriyat Yeyarim a Yahuda. Shi ya sa a ana kira wurin nan yamma da Kiriyat Yeyarim Mahane Dan har wa yau.
13
Daga can suka tafi ƙasar tudu ta Efraim suka zo gidan Mika.
14
Sa’an nan mutum biyar ɗin nan da suka leƙi asirin ƙasar Layish suka ce wa ’yan’uwansu, “Kun san cewa ɗaya daga cikin gidajen nan yana da efod, waɗansu allolin iyali, siffar da aka sassaƙa da kuma gunki na zubi? To, kun san abin da za ku yi.”
15
Saboda haka suka juya a wurin suka shiga gidan saurayin nan Balawe a wajen Mika suka gaishe shi.
16
Mutanen Dan ɗari shida da suka sha ɗamarar yaƙi suka tsaya a bakin ƙofa.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings