Mahukunta 17:7-13
7
Wani saurayi Balawe daga Betlehem a Yahuda, wanda yake zama cikin zuriyar Yahuda,
8
ya bar garin ya tafi neman inda zai zauna. A hanyarsa ya zo gidan Mika a ƙasar tudu ta Efraim.
9
Mika ya ce masa, “Daga ina kake?” Ya ce, “Ni Balawe ne daga Betlehem a Yahuda, ina kuwa neman wurin zauna ne.”
10
Sa’an nan Mika ya ce masa, “Ka zauna tare da ni ka zama mini mahaifi da firist, zan kuwa ba ka azurfa goma na shekel a shekara, tufafinka da kuma abincinka.” Sai Balawen ya tafi.
11
Saboda haka Balawen ya yarda ya zauna tare da shi, ɗan saurayin kuwa ya zama kamar ɗaya daga cikin ’ya’yansa.
12
Sa’an nan Mika ya naɗa Balawen, saurayin kuwa ya zama masa firist ya kuma zauna a gidansa.
13
Mika ya ce, “Yanzu na san cewa Ubangiji zai yi mini alheri, da yake Balawen nan ya zama firist nawa.”
Settings