Mahukunta 18:27-31
27
Sa’an nan suka ɗauko abin da Mika ya yi, da firist nasa, suka tafi Layish, suka fāɗa wa mutanen da suke zaman lafiya, ransu kuma a kwance. Suka fāɗa musu suka kuma ƙone birninsu.
28
Ba wanda zai cece su domin suna nesa da Bet-Sidon kuma ba sa hulɗa da kowa. Birnin yana a kwari kusa da Bet-Rekob. Mutanen Dan suka sāke gina birnin suka zauna a can.
29
Suka sa wa birnin suna Dan, wato, sunan kakansu Dan, wanda aka haifa wa Isra’ila, ko da yake a dā ana kira birnin Layish.
30
A can mutanen Dan suka kafa wa kansu gumaka, Yonatan ɗan Gershom, ɗan Musa, da ’ya’yansa maza firistoci ne na kabilar Dan har lokacin da aka kwashe mutane zuwa bauta.
31
Suka ci gaba da amfani da gumakan da Mika ya yi, a duk wannan lokacin gidan Allah yana a Shilo.
Settings