Mahukunta 18:14-26
14
Sa’an nan mutum biyar ɗin nan da suka leƙi asirin ƙasar Layish suka ce wa ’yan’uwansu, “Kun san cewa ɗaya daga cikin gidajen nan yana da efod, waɗansu allolin iyali, siffar da aka sassaƙa da kuma gunki na zubi? To, kun san abin da za ku yi.”
15
Saboda haka suka juya a wurin suka shiga gidan saurayin nan Balawe a wajen Mika suka gaishe shi.
16
Mutanen Dan ɗari shida da suka sha ɗamarar yaƙi suka tsaya a bakin ƙofa.
17
Sai mutum biyar da suka leƙi asirin ƙasar suka shiga ciki suka ɗauke gunkin da aka sassaƙa, efod, sauran allolin gida da kuma gunki na zubi yayinda firist ɗin tare da mutane ɗari shida da suka yi ɗamarar yaƙi suna tsaye a bakin ƙofa.
18
Sa’ad da waɗannan mutane suka shiga gidan Mika suka ɗauke gunkin da aka sassaƙa, efod, sauran allolin gida da kuma gunki na zubi, sai firist ya ce musu, “Me kuke yi?”
19
Suka ce, “Ka yi shiru! Kada ka ce wani abu. Zo tare da mu, ka zama mahaifinmu da kuma firist. Bai fi maka ka yi wa kabila da kuma zuriya a Isra’ila aikin firist ba, da ka bauta wa iyali guda kawai?”
20
Sai firist ya yi farin ciki. Ya ɗauki efod, sauran allolin gida da siffar da aka sassaƙa ya tafi tare da mutanen.
21
Suka sa ’ya’yansu ƙanana a gaba, dabbobinsu da mallakansu a gabansu, suka juya suka tafi.
22
Sa’ad da suka yi ɗan nisa daga gidan Mika, sai aka kira mutanen da suke maƙwabtakar da Mika suka taru suka bi mutanen Dan suka cim musu.
23
Da suna ihu suna binsu, sai mutanen Dan suka waiga suka cewa Mika, “Mece ce damuwarka da ka kira mutanenka su zo su fāɗa mana?”
24
Ya amsa ya ce, “Kun kwashe allolin da na yi, da kuma firist nawa, kuka tafi. Me kuma nake da shi? Yaya za ku ce, ‘Mece ce damuwata?’ ”
25
Mutanen Dan suka ce, “Kada ka kuskura ka ce kome, in ba haka ba mutanen nan za su harzuƙa, da kai da iyalinka duka ku rasa rayukanku.”
26
Saboda haka mutanen Dan suka kama hanyarsu, Mika kuwa da ya ga an fi ƙarfinsa, sai ya juya ya koma gida.
Settings