Yoshuwa 22:13-26
13
Saboda haka sai Isra’ilawa suka aiki Finehas ɗan Eleyazar, firist, zuwa ƙasar Gileyad, wurin mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.
14
Suka aiki shugabanni guda goma su tafi tare da shi, ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila, kowannensu shugaba ne a iyalansa.
15
Sa’ad da suka je Gileyad, wurin mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, sai suka ce musu,
16
“Dukan jama’ar Ubangiji sun ce yaya za ku juya wa Allah na Isra’ila baya haka? Yaya za ku daina bin Ubangiji ku gina wa kanku bagade, ku yi masa tawaye yanzu?
17
Zunubin da Feyor ya yi bai ishe mu ba ne? Ga shi, har yanzu ba mu gama tsarkakewa daga wannan zunubi ba, ko da yake annoba ta auko wa mutanen Ubangiji!
18
Yanzu za ku daina bin Ubangiji ne? “In kuka yi wa Ubangiji tawaye yau, gobe zai yi fushi da dukan mutanen Isra’ila.
19
Idan ƙasar mallakarku ƙazantacciya ce, sai ku haye zuwa ƙasar Ubangiji, inda tabanakul yake, mu zauna tare. Amma kada ku yi wa Ubangiji, ko kuma ku yi mana tawaye ta wurin gina wa kanku bagade wanda ba na Ubangiji Allahnmu ba.
20
Lokacin da Akan ɗan Zera ya yi rashin aminci game da kayan da aka keɓe, fushinsa Ubangiji bai auko a kan mutanen Isra’ila duka ba? Ai, ba shi kaɗai ya mutu don zunubinsa ba.”
21
Sai mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse suka amsa wa shugabannin iyalan Isra’ila suka ce,
22
“Maɗaukaki, Allah, Ubangiji! Maɗaukaki, Allah, Ubangiji ya sani! In mun yi wannan cikin tawaye ko rashin biyayya ga Ubangiji ne, kada ku bar mu da rai yau.
23
Idan mun bar bin Ubangiji, muka gina wa kanmu bagade don mu miƙa hadayun ƙonawa, ko kuwa hadayun gari, ko kuwa hadayun salama, to, bari Ubangiji kansa ya sāka mana.
24
“A’a! Mun yi haka ne don tsoro, kada nan gaba ’ya’yanku su ce wa ’ya’yanmu, ‘Me ya haɗa ku da Ubangiji, Allah na Isra’ila?
25
Ubangiji ya sa Urdun ya zama iyaka tsakaninmu da ku, ku mutanen Ruben da mutanen Gad! Ba ku da rabo cikin Ubangiji.’ ’Ya’yanku za su iya sa ’ya’yanmu su daina tsoron Ubangiji.
26
“Shi ya sa muka ce, ‘Bari mu yi shiri mu gina bagade, amma ba na ƙona hadayu ko na sadaka ba.’
Settings