1 Sama’ila 20:8-32
8
Kai kuma, ka nuna alheri ga bawanka, gama ka riga ka yi yarjejjeniya da ni a gaban Ubangiji, in kuwa na yi laifi ne sai ka kashe ni da kanka. Don me za ka bashe ni ga mahaifinka?”
9
Yonatan ya ce, “Labudda! In na ji ƙishin-ƙishin, cewa mahaifina yana neman yă kashe ka ashe, ba zan gaya maka ba?”
10
Dawuda ya ce, “Wa zai gaya mini idan mahaifinka ya amsa maka da amsa marar daɗi?”
11
Yonatan ya ce, “Zo mu fita zuwa fili.” Sai suka tafi tare.
12
Sai Yonatan ya ce wa Dawuda, “Na yi rantse da Ubangiji, Allah na Isra’ila cewa war haka jibi, zan yi ƙoƙari in ji daga mahaifina, idan ya yi magana mai kyau game da kai, zan gaya maka.
13
Amma in mahaifina ya sa zuciya yă cuce ka, Ubangiji yă hukunta ni da hukunci mai tsanani in ban gaya maka ba, in kuma sa ka ka tafi lafiya. Ubangiji yă kasance tare da kai kamar yadda ya kasance da mahaifina.
14
Amma ka nuna mini alheri marar ƙarewa iri ta Ubangiji dukan rayuwata don kada a kashe ni.
15
Kada kuma ka yanke alherinka ga iyalina ko da Ubangiji ya hallaka dukan maƙiyin Dawuda a duniya.”
16
Saboda haka Yonatan ya yi yarjejjeniya da gidan Dawuda cewa Ubangiji yă kawo dukan maƙiyin Dawuda ga mutuwa.
17
Yonatan kuwa ya sa Dawuda ya sāke tabbatar masa rantsuwansa game da abokantakarsa da shi, gama yana ƙaunar Dawuda kamar ransa.
18
Sai Yonatan ya gaya wa Dawuda cewa, “Gobe ne Bikin Sabon Wata, za a rasa ka, da yake kujerarka za tă kasance ba kowa a kai.
19
Jibi wajajen yamma, ka tafi wurin da ka ɓuya lokacin da wannan matsala ta fara, ka tsaya kusa da dutsen Etsel.
20
Zan harbi kibiya uku ta wajen, sai ka ce dai ina harbin baka.
21
Sa’an nan zan aiki yaro in ce masa, ‘Je ka nemo kibiyoyin.’ In na ce masa, ‘Duba, kibiyoyin suna wannan gefen da kake, kawo su,’ sai ka fito, wato, tabbatacce muddin Ubangiji yana raye, ka tsira, ba wani hatsari.
22
Amma in na ce wa yaron, ‘Duba, kibiyoyin suna gaba da kai,’ sai ka tafi, gama Ubangiji ya sallame ka.
23
Game da al’amarin da muka tattauna da ni da kai kuwa, ka tuna fa Ubangiji ne shaida tsakanina da kai har abada.”
24
Dawuda ya tafi ya ɓuya a fili. Sa’ad da ranar Bikin Sabon Wata ta zo, sarki ya zauna don yă ci.
25
Ya zauna a kujeransa inda ya saba zama kusa da bango yana fuskantar Yonatan, Abner kuma ya zauna kusa da sarki. Amma kujeran Dawuda ba kowa.
26
Shawulu bai ce kome ba a ranar domin ya yi tsammani wataƙila wani abu ya faru da Dawuda ya mai da shi marar tsarki, tabbatacce ba shi da tsarki.
27
Amma kashegari, rana ta biyu ga wata, kujeran Dawuda kuma ba kowa, sai Shawulu ya ce wa ɗansa Yonatan, “Me ya sa ɗan Yesse bai zo cin abinci, jiya da yau ba?”
28
Yonatan ya ce, “Dawuda ya nemi izinina don yă tafi Betlehem.
29
Ya ce, ‘Bari in tafi gama iyalinmu suna miƙa hadaya a gari, ’yan’uwana kuwa sun gayyace ni in kasance a can. In na sami yardarka, bari in tafi in ga ’yan’uwana.’ Dalilin ke nan da bai zo ci da sarki ba.”
30
Fushin Shawulu ya ƙuna a kan Yonatan, sai ya ce masa, “Kai shege ne, haihuwar banzan mace; ai, na san kana goyon bayan ɗan Yesse don ka wulaƙantar da kanka da mahaifinka.
31
Muddin ɗan Yesse yana da rai a duniya, ba za ka kahu ba. Sarautarka kuma ba za tă kahu ba. Yanzu sai ka je ka kawo mini shi. Dole yă mutu.”
32
Yonatan ya ce wa mahaifinsa, “Me ya sa zai mutu? Me ya yi?”
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings