Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Zechariah

36 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Danginsu bisa ga iyalansu da aka jera bisa ga tarihin zuriyarsu su ne, Yehiyel shi ne sarki, akwai Zakariya,

  2. Zakariya ɗan Meshelemiya shi ne mai tsaro a mashigin Tentin Sujada.

  3. Tare da su kuma ’yan’uwansa da suke biye bisa ga matsayi. Wato, Zakariya, Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ben, Ma’asehiya, Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom da Yehiyel, matsaran ƙofofi.

  4. Zakariya, Aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ma’asehiya da Benahiya, ne za su kaɗa molaye masu murya sama-sama, bisa ga alamot.

  5. Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zakariya, Benahiya da Eliyezer firistoci, su ne za su busa ƙahoni a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-Edom da Yehiya su ma za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin.

  6. Asaf shi ne babba, sai Zakariya na biye, sa’an nan Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benahiya, Obed-Edom da Yehiyel. Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna,

  7. Ɗan’uwan Mika shi ne, Isshiya; daga ’ya’yan Isshiya maza, Zakariya.

  8. Meshelemiya yana da ’ya’ya maza. Zakariya ɗan fari, Yediyayel na biyu, Zebadiya na uku, Yatniyel na huɗu,

  9. Hilkiya ne na biyu, Tabaliya ne na uku sai kuma Zakariya na huɗu. ’Ya’ya da dangin Hosa su 13 ne duka.

  10. Ƙuri’a don Ƙofar Gabas ta fāɗo a kan Shelemiya. Sai aka jefa ƙuri’u don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma’ana, sai ƙuri’a ta ƙofar arewa ta fāɗo a kansa.

  11. bisa ɗayan rabi kabilar Manasse a Gileyad shi ne, Iddo ɗan Zakariya; bisa mutanen Benyamin shi ne, Ya’asiyel ɗan Abner;

  12. A shekara ta uku ta mulkinsa, ya aiki ma’aikatansa Ben-Hayil, Obadiya, Zakariya, Netanel da Mikahiya su yi koyarwa a garuruwan Yahuda.

  13. Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kan Yahaziyel ɗan Zakariya, ɗan Benahiya, ɗan Yehiyel, ɗan Mattaniya, wani Balawe kuma zuriyar Asaf, yayinda yake tsaye a cikin taron.

  14. ’Yan’uwan Yehoram, ’ya’yan Yehoshafat maza su ne, Azariya, Yehiyel, Zakariya, Azariyahu, Mika’ilu da Shefatiya. Dukan waɗannan su ne ’ya’yan Yehoshafat sarkin Isra’ila maza.

  15. Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Zakariya ɗan Yehohiyada firist. Ya tsaya a gaban mutane ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, ‘Me ya sa ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji ba? Ba za ku yi nasara ba. Domin kun yashe Ubangiji, shi ma ya yashe ku.’ ”

  16. Amma suka yi masa maƙarƙashiya, kuma ta wurin umarnin sarki suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu a filin haikalin Ubangiji.

  17. Sarki Yowash bai tuna da alherin da Yehohiyada mahaifin Zakariya ya nuna masa ba, sai ya kashe ɗansa, wanda ya ce yayinda yake mutuwa, “Bari Ubangiji yă dubi wannan yă kuma sāka maka.”

  18. Sa’ad da Arameyawa suka janye, suka bar Yowash da mummunan rauni. Hafsoshinsa suka haɗa baki a kansa saboda kisan ɗan Yehohiyada firist da ya yi, suka kashe shi a kan gadonsa. Ta haka ya mutu aka kuma binne shi makabartan sarakuna.

  19. Ya nemi Allah a kwanakin Zakariya, wanda ya koyar da shi a tsoron Allah. Muddin ya nemi Ubangiji, Allah ya ba shi nasara.

  20. Daga zuriyar Elizafan, Shimri da Yehiyel. Daga zuriyar Asaf, Zakariya da Mattaniya.

  21. Mutanen fa suka yi aiki da aminci. Shugabanninsu, su ne Yahat da Obadiya, Lawiyawa zuriyar Merari da Zakariya da Meshullam, zuriyar Kohat. Dukan Lawiyawa waɗanda suke gwanaye a kayan kiɗi,

  22. Fadawansa su ma suka ba da taimako da yardar rai ga mutane da kuma firistoci da Lawiyawa. Hilkiya, Zakariya da Yehiyel masu aiki a haikalin Allah, suka ba firistoci hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyu da ɗari shida da kuma shanu ɗari uku.

  23. ɗan zuriyar Shekaniya ne shugaba, daga zuriyar Farosh, Zakariya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 150;

  24. daga Bebai, Zakariya ɗan Bebai ne shugaba, tare da shi akwai mutum 28;

  25. Saboda haka sai na aika a kira Eliyezer, da Ariyel, da Shemahiya, da Elnatan, da Yarib, da Natan, da Zakariya, da Meshullam waɗanda su ne shugabanni. Na kuma sa a kira Yohiyarib da Elnatan waɗanda masana ne.