Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Years: Length of, during the patriarchal age
Ayoyi game da Length of, during the patriarchal age
A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe.
Ruwa ya mamaye duniya har kwana ɗari da hamsin.
Ruwan ya janye a hankali daga ƙasa. A ƙarshen kwanaki ɗari da hamsin ɗin, ruwan ya ragu.
A rana ta fari ga wata na fari wanda Nuhu ya cika shekaru 601, ruwa ya shanye a ƙasa. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya ga cewa doron ƙasa ya bushe.