Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Token: Miracles of Moses, of the divine authority of his missions
Ayoyi game da Miracles of Moses, of the divine authority of his missions
Musa ya amsa ya ce, “In ba su gaskata ni ba, suka kuma ce, ‘Ubangiji bai bayyana gare ka ba fa’?”
Sai Ubangiji ya ce, “Mene ne wannan a hannunka?” Musa ya amsa ya ce, “Sanda.”
Sai Ubangiji ya ce, “Jefa shi ƙasa.” Musa ya jefa shi ƙasa, sai sandan ya zama maciji, Musa kuwa ya gudu daga gare shi.
Sai Ubangiji ya ce masa, “Sa hannunka ka ɗauke shi ta wutsiya.” Sai Musa ya miƙa hannu, ya kama macijin, macijin kuwa ya dawo sanda a hannunsa.
Ubangiji ya ce, “Wannan zai sa su ba da gaskiya cewa Ubangiji, Allah na kakanninsu, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da kuma Allah da Yaƙub, ya bayyana gare ka.”
Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Sa hannunka cikin rigarka.” Sai Musa ya sa hannunsa cikin rigarsa, sa’ad da ya fitar da shi, sai hannun ya a kuturce fari fat, kamar ƙanƙara.
Sai Ubangiji ya ce, “Yanzu, mayar da hannunka a rigarka.” Sai Musa ya sa hannunsa cikin rigarsa, da ya fitar da shi, sai hannun ya koma kamar sauran jikinsa.
Sa’an nan Ubangiji ya ce, “In ba su gaskata ba, ko kuma ba su kula da mu’ujiza ta fari ba, wataƙila su gaskata da ta biyun.
Amma in ba su gaskata mu’ujizan nan biyu ba, ko kuwa ba su saurare ka ba, sai ka ɗibo ruwa daga Nilu, ka zuba a busasshiyar ƙasa. Ruwan da ka ɗebo daga kogin zai zama jini a ƙasar.”